Yanzu-yanzu: Dakarun soji sun harbe kwamandan Boko Haram, Abu Imrana

Yanzu-yanzu: Dakarun soji sun harbe kwamandan Boko Haram, Abu Imrana

Kwamandan Boko Haram, Abu Imrana ya rasa ransa sakamakon musayar wutar da ta shiga tsakanin mayakan ta'addancin da dakarun sojin Najeriya a jihar Borno.

Wata majiya daga jami'an tsaro ta bayyana hakan ga jaridar The Cable a ranar Litinin.

Ta ce Imrana na daga cikin manyan kwamandojin da dakarun suka halaka, lamarin da ya girgiza 'yan ta'addan don yana daga cikin shugabanni masu rinjaye.

Boko Haram ta sabunta hare-harenta ga dakarun sojin Najeriya da ke yankin arewa maso gabas a cikin kwanakin nan.

A kalla mutum 150 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram a kananan hukumomin Monguno da Gubio na jihar Borno a makon da ya gabata.

Wani soja da dan sanda da mayakan Boko Haram din suka yi garkuwa da su a makonni biyu da suka gabata, an yi musu yankan rago a gaban 'yan kungiyar.

Majiyar ta ce marigayin kwamandan ne mashiryin hare-haren Monguno, Gubio da Nganzai.

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng