Har yanzu buɗe makarantu akwai haɗari - PTF

Har yanzu buɗe makarantu akwai haɗari - PTF

Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona, ya gargadi gwamnatocin jihohi da su jingine kudirin buɗe makarantu tukunna.

Kwamitin ya yi gargadin cewa, har kawo yanzu, akwai babban haɗari muddin aka buɗe makarantu a fadin tarayyar kasar nan.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni cikin birnin Abuja.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, wasu gwamnoni a Najeriya sun fara yunkurin buɗe makarantu domin dalibai su koma aji wajen daukan darasi.

"PTF ta na kira ga gwamnatocin jihohi da su fara gwajin al'umma, tare da shata ka'idojin kare kai daga kamuwa da cutar korona musamman bayar da tazara da kiyaye dokar nesa-nesa da juna."

"Mun samu rahoto cewa wasu jihohi sun fara tunanin buɗe makarantu, gidajen kallo da sauran wuraren tarurrukan jama'a."

"Har yanzu muna kira da babbar murya cewa, akwai babban haɗari muddin aka aiwatar da hakan, saboda haka ya kamata gwamnoni su sake yin dogon nazari gami da yin taka tsan-tsan."

"Akwai bukatar gwamnatocin jihohi su kiyaye dukkanin sharudan da muka shata yayin yanke duk wata shawara da za ta bai wa al'ummar damar sararawa."

Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Legit.ng ta ruwaito cewa, yayin da ake ci gaba da hurowa gwamnati wutar bude makarantu, masu ruwa da tsaki a sashen ilimi da na lafiya sun gargadi gwamnatin a kan kada ta yi gaggawar aiwatar da hakan.

Bayan ci gaba da sassauta dokar kulle da gwamnatin ke yi, masu ruwa da tsaki a sashen ilimi da kiwon lafiya sun fayyace alkibilar da suka fuskanta dangane da bude makarantu.

Masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi da kiwon lafiya, sun gargadi gwamnatin tarayya da ta jihohi a kan ka da su yi gaggawar bude makarantu a yanzu.

Da ta ke gargadin gwamnatin dangane da yunkurinta kan lamarin komawar dalibai makarantu, kungiyar Likitocin Najeriya NMA, ta ja kunnen gwamnatin da ta yi taka tsan-tsan.

KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yana ganawar sirri da gwamnan jihar Borno

Kungiyar NMA ta ja hankalin gwamnatin a kan kada ta kuskura ta bude makarantu a yanzu domin hakan zai iya mayar musu da hannun agogo baya a fafutikar da ake na dakile yaduwar cutar korona a kasar.

Shugaban kungiyar NMA, Farfesa Innocenta Ujah, ya ce har ila yau akwai sauran rina a kaba dangane da lamarin yaki da cutar korona a kasar nan.

Haka kuma kungiyoyin malamai da iyayen dalibai na Najeriya, NAPTAN da NUT, sun gargadi gwamnatin da ta yi dogon nazari da daukan matakai gabanin yanke shawarar bude makarantu.

Kungiyoyin biyu sun ankarar da gwamnatin a kan ka da ta yanke wani hukunci a yanzu wanda daga bisani za ta yi da na sanin zartar da shi a lokaci na gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel