Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yana ganawar sirri da gwamnan jihar Borno

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yana ganawar sirri da gwamnan jihar Borno

A yanzu haka mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana gudanar da wata ganawar sirri tare da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Wannan rahoto ya fito ne kai tsaye daga fadar shugaban kasa da Yammacin ranar Litinin, 15 ga watan Yuni.

Ganawar na gudana ne a fadar shugaban kasa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Hadimin shugaban kasa a kan sabuwar hanyar sadarwa ta zamani, Bashir Ahmad, shi ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta.

Buhari da Zulum a fadar shugaban kasa
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Buhari da Zulum a fadar shugaban kasa Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Akwai yiwuwar gwamna Zulum ya ziyarci shugaba Buhari har fada ne domin su tattauna kan sha'anin matsalar tsaro da ya addabi yankin Arewa maso Gabas.

A baya bayan nan ne Buhari yi tir da mummunar harin kisan kiyashi da aka kai kauyen Gubio da ke jihar Borno, inda aka kashe akalla mutum 81.

Shugaba Buhari ya ce wannan kisa da mayakan Boko Haram suka yi wa mutanen kauyen Gubio ya girgiza shi matuka.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Likitoci, iyaye da malamai sun gargadi gwamnatin a kan kada ta bude makarantu

A sanadiyar hakan shugaban kasar ya umarci dakarun Sojin Najeriya da su gaggauta ceto wadanda aka yi garkuwa da su da kuma shanun da aka sace.

Mummunan harin ya auku kwanaki kadan bayan da babban Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Buratai ya ziyarci fadar shugaban kasa.

Laftanar Janar Buratai yayin ziyararsa ya shaida wa shugaba Buhari, cewa sauran kiris dakarun Najeriya su ga bayan mayakan Boko Haram karkaf.

A yayin haka ne dai shugaba Buhari ya ce zai saurari cikakken bayanin abinda ya faru daga gwamnan bayan ya kai ziyarar jaje da kuma gani da ido wadannan wurare.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamna Zulum ya garzaya wannan kauye na Gubio bayan samun labarin wannan hari da aka kai kauyen.

A ranar Laraba, 10 ga wata Yuni, Gwamna Zulum ya tabbatar da kisan mutane 81 da jana'izarsu sakamakon harin da mayakan Boko Haram suka kai a ranar Talata.

Zulum ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a garin Felo da ke karkashin karamar hukumar Gubio inda harin ya faru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel