Kasashe 8 masu karfin tattalin arziki a Afrika

Kasashe 8 masu karfin tattalin arziki a Afrika

- A 2019 an yi kiyasin cewa Najeriya ce ke ta fi kowacce kasa karfin tattalin arziki a Afrika da $444.916 biliyan

- Kasashe irinsu Algeria, Angola da Morocco ne a matakai na hudu, bakwai da biyar

- Kasar Afrika ta Kudu da Egypt ne suka bayyana da $371.298 biliyan da $299.589 biliyan

Najeriya ce ta daga a kasashe masu karfin tattalin arziki a dukkan Afrika a 2019 kamar yadda Africa Facts Zone ta wallafa.

A wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter a ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni, Najeriya ce ke kan gaba da karfin tattalin arziki da ya kai $444.916 biliyan.

Kasar Afrika ta Kudu ce ta bayyana a ta biyu da $371.29 biliyan yayin da Egypt ta kai mataki na uku da $299.589 biliyan.

Kasar Kenya na a ta hudu da $99.246 biliyan, Angola ta biyar da $92.191 biliyan sai kuma Ethiopia da ke da $90.968.

KU KARANTA: Abubuwa 6 masu bada mamaki game da Najeriya

Kasashe 8 masu karfin tattalin arziki a Afrika
Kasashe 8 masu karfin tattalin arziki a Afrika. Hoto daga Al-Jazeera
Asali: Twitter

A wani labari na daban, annobar korona ta shafi duk wani bangare na tattalin arzikin duniya da kasuwanci. Amma duk da haka, mujallar Forbes ta wallafa manyan masu kudi a duniya da suka kai 2,095.

Ga manyan masu kudin duniya da takaitaccen bayani a kansu.

1. Jeff Bezos: Dan asalin kasar Amurka ne kuma ya samu kudinsa ta fasahar Amazon. Bezos ya mallaki dukiya da ta kai $113 biliyan. Shine ya fi kowanne mahaluki kudi a duniya a shekarar 2020.

2. Bill Gates: Dan asalin kasar Amurka ne kuma shi ke da fasahar Microsoft. Bill Gates ya mallaki dukiyar da ta kai $98 biliyan kuma shine mutum na biyu da ya fi kowa arziki a duniya a 2020.

3. Bernard Arnault & Family: Hamshakin mai kudin ya mallaki dukiyar da ta kai $76 biliyan kuma dan kasar Faransa ne.

4. Warren Buffett: Hamshakin mai arzikin ya mallaki dukjya da ta kai $67.5 biliyan. Dan asalin kasar Amurka ne mamallakin Berkshire Hathaway Finance & Investment.

5. Larry Ellison: Mai tarin dukiya ne da ya bayyana a mataki na biyar a fadin duniya. Ya mallaki dukiyar da ta kai $57 biliyan. Dan asalin kasar Amurka ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel