Abubuwa 6 masu bada mamaki game da Najeriya

Abubuwa 6 masu bada mamaki game da Najeriya

Duk da manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta, akwai wasu abubuwan bada mamaki game da kasar da ke nahiyar Afrika wacce ta sa kasashe ke mata kallon wacce ta fita zarra a duniya.

A yayin da kasar ke murnar zagayowar ranar damokaradiyya a yau Juma'a, 12 ga watan Yuni, Legit.ng ta kawo muku abubuwa shida masu bada mamaki game da Najeriya.

1. Najeriya ce kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a fadin nahiyar Afrika.

2. Najeriya ce kasa ta biyu a dukkan Afrika da ke kan gaba a fitar da kayanta kasashen ketare don siyarwa.

3. Najeriya ce kasa ta biyar a Afrika da ta fi kowacce yawan kudi a asusun ajiyar kasashen waje.

4. Najeriya ce kasar da fi kowacce kasa a Afrika samarwa tare da fitar da kayayyakin man fetur.

5. Masana'antar fina-finai ta kudancin Najeriya (Nollywood) ita ce masana'antar fim ta uku a girma a fadin duniya.

6. Masana'antar wakar kasar nan tana daya daga cikin masana'antun waka mafi shahara a fadin duniya baki daya.

KU KARANTA: Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo)

A wani labari na daban, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce shugabannin siyasan Najeriya har hanzu sun yi kasa a gwiwa wajen farantawa yan Najeriya rai.

A sakon murnar zagayowar ranar demokradiyya, Atiku, ya ce akwai masu baiwa da dama a Najeriya amma rashin shugabancin kwarai ya hana ganosu.

A watan Yunin 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan dokar mayar da 12 ga Yuni, ranar murnar demokradiyya a Najeriya.

Gabanin yanzu, ranar 29 ga Mayu ake murnar demokradiyya.

Tsohon shugaban kasan ya ce duk da cewan shugabannin Najeriya sun yi iyakan kokarinsu wajen bayar da shugabancin kwarai tun 1999, har yanzu da saura.

Yace: "Murnar ranar Demokradiyya nuna tabbacin irin jajircewanmu ne kan kafa gwamnatin demokradiyya da amincewa da doka."

"Kamar da ya marigayi Bashorun MKO Abiola ke cigaba da zama jarumin gwagwarmayan 12 ga Yuni, akwai ire-irensa irinsu Cif Alfred Rewane; Tafida Shehu Musa Yar’Adua, Alhaja Kudirat Abiola, dss."

"Amma duk da cewa mun zabi rana na musamman domin murnar demokradiyya, akwai takaici har yanzu mun gaza yiwa al'ummarmu hallaci."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel