Adana kudi Abacha ya yi a kasashen ketare don kada mu jigata - Al-Mustapha

Adana kudi Abacha ya yi a kasashen ketare don kada mu jigata - Al-Mustapha

Hamza Al-Mustapha ya ce marigayi Sani Abacha da ya rasu a 1998 ya adana kudade a kasashen ketare ne yadda 'yan Najeriya ba za su jigata ba.

An samo sama da $3.624 biliyan da Abacha ya wawure daga kasashe hudu tsakanin 1998 zuwa 2020.

A watan da ya gabata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a kalla an wawure kusan dala biliyan daya a karkashin mulkin Sani Abacha daga Najeriya.

A yayin zantawa da BBC a ranar Alhamis, Al-Mustapha, wanda ya yi aiki a matsayin babban dogarin Abacha, ya ce dankara kudaden da aka yi a bankunan ketare yayin mulkin Abacha hukunci ne da masu ruwa da tsaki a lokacin suka yanke.

"Na ce akwai lokacin da Najeriya za ta fuskanci hukunci. An yi wannan tsarin ne don gujewa jigatar Najeriya da 'yan Najeriya idan lokacin ya zo," yace.

"Mun tattara sarakunan gargajiya daga Kudu da arewa tare da manyan mutane na wannan lokacin, na gwamnati da wadanda basu gwamnati.

"Mun yi taron ne a wani wuri da ake kira da Camp Bassey Officer's Mess da ke Brigade Guards. A nan ne muka tattauna a kan hukuncin da Najeriya za ta iya fuskanta.

Adana kudi Abacha ya yi a kasashen ketare don kada mu jigata - Al-Mustapha
Adana kudi Abacha ya yi a kasashen ketare don kada mu jigata - Al-Mustapha. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo)

"Ina mamakin yadda ake bata wa Abacha suna. Ina matukar mamaki saboda koda ya hau mulki, Najeriya na da kasa da dala biliyan biyu a asusunta na kasashen ketare.

"Amma a cikin shekaru hudu da watanni takwas, asusunmu ya kai $9 biliyan. Bayan mutuwarsa da watanni tara, dukkan kudaden sun bace.

"Bawan Allah da ya daga darajar Najeriya da inganta tsaronta shine yanzu ake zagi. Amma wadanda suka wawure kudin tare da rabawa suna nan suna walwalarsu."

Al-Mustapha ya kara da cewa, jarumi Abacha ya tsallake juyin mulki takwas.

"Yan Najeriya sun san da juyin mulki uku kadai da Abacha ya tsallake amma gaskiya takwas ne. Ya rasu a lokacin da ake shirya na takwas din," yace.

A baya, manjo din mai murabus ya ce Allah kadai zai iya sakawa Abacha a kan kokarin da yayi a kan Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel