Coronavirus: Jihar Kano ta samu sabbin cibiyoyin gwaji guda 2
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya kaddamar da wasu sabbin cibiyoyin gwajin cutar korona guda biyu don haɓaka ƙarfin gwaji a jihar.
Gwamnatin Kano ta kaddamar da cibiyoyin gwajin tare da hadin gwiwar gidauniyar nan mai yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya, International Foundation Against Infectious Disease in Nigeria (IFAIN).
Kafin wannan lokaci, cibiyoyin gwajin cutar korona guda uku ne kawai suke aiki a jihar Kano da suka hadar wadda ta ke Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano.
Sai kuma cibiyar bincike kan cututtuka masu yaduwa ta Jami'ar Bayero da kuma Asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A yayin da akwai kusan mutane miliyan 20, cibiyoyin gwaji uku kadai ba za su iya wadatar da jihar Kano ba wajen ci gaba da kula da yaduwar cutar a fadin jihar.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
KARANTA KUMA: Sarkin Katsina ya naɗa mai yiwa ƙasa hidima sabon hakimin 'Yantumaki

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Sabuwar cibiyar gwajin da ke kan titin Independence a Unguwar Bompai ta jihar Kano, ta na da ƙarfin ikon yi wa mutum 300 gwaji a duk rana.
Cikin sanarwar da ta fito daga bakin sakataren sadarwa na fadar gwamnatin Kano, Malam Abba Anwar, ya ce daya daga cikin cibiyoyin gwajin da aka kaddamar ta na dauke da gadajen jinya 300.
Haka kuma cibiyar gwajin da gidauniyar IFAIN ta samar, ta na da ikon yi wa mutum 90 gwajin kwayoyin cutar korona a kowace rana kamar yadda hadimin gwamnan ya sanar.
Da ya ke gabatar da jawabai yayin kaddamar da cibiyoyin, Gwamna Ganduje ya nemi hadin gwiwar duk masu da tsari domin samun nasara a kan kalubalen da ke tattare da annobar korona.
Idan ba a manta ba a makon da muke ciki ne gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin kan yawan mace-macen da aka rika samu a jihar Kano a watanni baya.
Gwamnatin ta ce kashi 50 zuwa 60 cikin dari na mace-macen da aka samu a jihar Kano tsakanin watan Afrilu zuwa Mayu, sun ta'allaka ne da harbin cutar korona.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng