Sarkin Katsina ya naɗa mai yiwa ƙasa hidima sabon hakimin 'Yantumaki

Sarkin Katsina ya naɗa mai yiwa ƙasa hidima sabon hakimin 'Yantumaki

Mai Martaba Sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir Usman, ya nada Atiku Abubakar Atiku, a matsayin sabon Hakimin 'Yantumaki a karamar hukumar Danmusa ta jihar.

Sabon Hakimin shi ne babban ɗan marigayi Atiku Abubakar, tsohon Hakimin 'Yantumaki da 'yan ta'adda suka kashe har cikin fadarsa a makon da ya gabata.

Sakataren fadar masarautar Katsina wanda kuma ya kasance mai rike da rawanin Sallaman Katsina, shi ne ya tabbatar da hakan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce sabon dagacin a halin yanzu ya na cikin yi wa ƙasa bauta ne a karkashin shirin Hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC.

Legit.ng ta ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun harbe Hakimin 'Yantumaki, Maidabino, har lahira cikin fadarsa a safiyar ranar Litinin, 1 ga watan Yuni.

Mai Martaba Sarkin Katsina; Abdulmumin Kabir Usman
Mai Martaba Sarkin Katsina; Abdulmumin Kabir Usman
Asali: UGC

An ruwaito cewa 'yan ta'addan sun kai harin ne haye a kan babura da misalin karfe 12 na dare inda suka rika harbe-harben iska domin razana mutanen kauyen.

Daga bisani 'yan bindigar sun shiga cikin fadar inda suka kashe Hakimin nan take kuma suka raunata daya daga cikin dogarawansa.

Haka kuma mun jin cewa, fusatattun matasa a ranar Talata sun tare titin ‘Yantumaki, bayan mahara sun sace wani jami’in kiwon lafiya tare da ‘yar sa a garin.

Jami’in mai suna Mansur Yusuf, an yo masa takakkiya ne har gida kuma aka arce da shi, makonni biyu bayan kashe Hakimin garin.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta yi barazanar bayar da sammacin kama Lai Mohammed da wasu ministoci

Sashen Hausa na jaridar Premium Times ya ruwaito cewa, mazauna garin Danmusa sun ce Mansur Yusuf makwabcin Hakimin ne.

Matasan dai sun yi tururuwar fitowa kan tituna domin gudanar da zanga-zanga saboda matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da tabarbarewa.

Sun yi ta surfa wa Gwamnatin Jihar Katsina da ta Tarayya zagi, domin nuna matukar bacin ransu game da halin ko-in-kula da suke zargi shugabannin suna yi kan batun tsaron jihar.

Babu shakka a baya bayan matsalar rashin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman a jihar Katsina da Zamfara.

Kungiyar bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin kasar cikin shekaru 10.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel