Majalisar Dattawa ta yi barazanar bayar da sammacin kama Lai Mohammed da wasu ministoci

Majalisar Dattawa ta yi barazanar bayar da sammacin kama Lai Mohammed da wasu ministoci

Majalisar dattawa ta yi barazanar bayar da sammacin kama Ministan Labarai da Al’adu; Alhaji Lai Mohammed, Karamin Ministan Man Fetur; Timipre Sylva da kuma Ministan Wuta; Engr. Saleh Mamman.

Majalisar ta ce za ta bayar da sammacin cafke ministocin uku saboda sun ki amsa goron gayyatar da ta ba su na neman su yi bayani a kan duk wani shige-da-fice na batar da kudi a ma'aikatunsu.

Shugaban kwamitin kula da kudin al'umma a majalisar, Sanata Matthew Urhoghide na jam'iyyar PDP mai wakiltar shiyar Edo ta Kudu, shi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.

Urhoghide ya ce majalisar ba za ta yi jinkirin yin amfani da karfin ikonta ba wajen ba da sammacin damko duk wadanda suka ki amsa goron gayyatar ta.

Ya ce abin kunya ne kuma abin takaici a ce wasu daga cikin masu rike da ma'aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnatin su na kin amsa kiranta ba yayin da ta nemi bukatar hakan.

Sanatan ya ce ya kamata duk wanda aka nema ya yi bayani kan kudaden da suke shige-da fice a ma'aikatar da suke jagoranta su kwantar da kai domin aiwatar da hakan cikin salama.

Buhari da Ministoci a dakin taro na fadar shugaban kasa
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Buhari da Ministoci a dakin taro na fadar shugaban kasa Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

Ya ce a yanzu kwamitin ba ya da wani zabi face ya yi amfani da karfin iko wajen tursasawa duk wadanda suka ki amsa kiran majalisar a bisa tanadin sashe na 89 cikin kundin tsarin mulki.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Sanatan yana cewa, muddin wadanda suka ki amsa kiran majalisar basu yi hattara ba, za a nemi su bayyana ta karfi kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Sauran wadanda majalisar ta yi barazanar kamawa saboda sun yi wa kiran da ta yi musu kunnen uwar shegu, sun hadar da Ministar Harkokin Mata, Mrs Pauline Tallen.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta shata matakai 11 na sassauta dokar kulle a mataki na gaba

Haka kuma takwaranta na Ma'aikatar Albarkatun Kasa; Arc. Olamilekan Adegbite da kuma shugaban Hukumar Kidaya na Kasa; Eze Duruihuoma.

Ya ce "tsawon wata guda kenan aka aike musu da wasikar goron gayyata domin su yi bayani a kan rahoton da Ofishin binciken kudi na kasa ya fitar a shekarar 2015."

"Amma da gangan kuma saboda rashin sanin ya kamata, sun ki amsa gayyatarmu. Rashin bayyanarsu a gaban wannan Kwamiti ya kasance rashin yi wa madafun iko ladabi."

A yayin ci gaba da bayyana bacin ransa kan wannan koma baya, Sanata Urhoghide ya ce "rashin bayyanarsu a gaban kwamitin shi ke sa wa ana zargin majalisun tarayya ba sa sauke nauyin da rataya a wuyansu."

"A Najeriya ne kadai mutane za su kashe kudaden gwamnati kuma suka gaza su fitowa domin yin bayani dalla-dalla kan abin da suka kashe."

A cewarsa, galibin Ministocin sun bayar da uzurirrika masu rauni kuma marasa karfi ko wani tushe, a yayin bayyana dalilan da suka hana su bayyana a gaban majalisar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel