Coronavirus: Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta shata matakai 11 na sassauta dokar kulle a mataki na gaba

Coronavirus: Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta shata matakai 11 na sassauta dokar kulle a mataki na gaba

A yayin ci gaba da sassauta dokar kulle a fadin tarayya domin bai wa al'umma damar samun sukuni, gwamnatin tarayya ta shata wasu sabbin sharaɗi da za a kiyaye a mataki na gaba.

Gwamnatin tarayya ta fitar da wasu jerin sharuɗa da za a kiyaye yayin da adadin mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya ya kai dubu goma sha uku da 873.

Cikin wani sako da ma'aikatar lafiya ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, ta wassafa sharuɗan da za a kiyaye yayin sassauta dokar kulle a matakin gaba.

Ta bayyana cewa za a umarci hukumomin tsaro su tabbatar da an kiyaye sharuɗan a duk hanyoyin da suka dace.

Ana iya tuna cewa, gwamnatin tarayya a ranar Litinin, 1 ga watan Yuni, ta ba da sanarwar sassauta dokar kulle, inda ta ba da umarnin bude dukkan masallatai da majami'u.

Gwamnatin tarayya kamar yadda jaridar Legit.ng ta ruwaito, ta yanke hukuncin hakan ne bayan karbar shawarwarin da kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona ya ba ta.

Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Haka kuma gwamnatin ta ba da sanarwa cire dokar tashin jiragen saman cikin gida daga ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, inda ake sa ran za ta cire dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi.

A halin yanzu an ci gaba da sassauta dokar kullen daki-daki inda al'amuran yau da kullum suka fara dawo sannu a hankali.

Gwamnatin ta kuma sanya kotun tafi-da-gidanka a duk jihohin tarayyar kasar domin hukunta duk wanda ya sabawa sharuɗan da ta gindaya.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Osinbajo ya gabatar da tsare-tsaren yadda Najeriya za ta farfado da tattalin arziki

A mataki na gaba da gwamnatin ta yi yunkurin sassauta dokar kullen wadda gwamnoni 36 na Najeriya suka aminta da su, ta shata sabbin sharuɗa 11 kamar haka:

1. Wajibi ne yin amfani da takunkumin rufe fuska a wuraren taron jama'a.

2. Tanadar sunadarin wanke hannu (sanitizer) da wuraren wanke hannu a karkashin ruwa mai gudana.

3. Dole ne sai an rika kiyaye dokar nesa-nesa da juna da bayar da tazara, kuma kada wani taron jama'a ya haura na mutum 20.

4. Dole ne a ci gaba da kiyaye dukkanin sharuɗan da aka gindaya a wuraren bauta.

5. Wajibi ne a shimfida matakan takaita yawan mutane a kasuwanni tare da kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta.

6. Za a iya bude Otel amma wuraren cin abinci za su ci gaba da kasancewa a rufe.

7. Bankuna da sauran kamfanoni da masana'antu za su iya ci gaba da ayyukansu kamar yadda suka saba a baya.

8. Ma'aikatun gwamnati za su bude daga karfe 9.00 na safe zuwa 2.00 na rana daga Litinin zuwa Juma'a.

9. Makarantu, Mashaya, da sauran wuraren shakatawa za su ci gaba da kasancewa a rufe.

10. Akwai dokar takaita zirga-zirga a fadin tarayyar kasar daga karfe 10.00 na dare zuwa 4.00 na Asuba.

11. Jigilar jiragen saman cikin gida za ta dawo amma an haramta tashin jiragen saman kasa-da-kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel