Majalisa ta amince da kasafin kudin 2020 da aka yi wa kwaskwarima

Majalisa ta amince da kasafin kudin 2020 da aka yi wa kwaskwarima

Majalisar dattawa a ranar Alhamis, ta amince da kwaskwarimar da aka yi wa kasafin kudin Najeriya na bana wanda aka kasafta za a kashe Naira tiriliyan 10.8.

Sakamakon annobar korona da kuma karyewar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya, ya sanya gwamnati ta yi wa kasafin kudin kasar sauyin fasali babu shiri.

Haka kuma raguwar samun kudaden shiga da gwamnatin ta yi hasashe gami da faduwar darajar naira, ya sanya aka yi wa kasafin na bana kwaskwarima.

Tun a watan Maris ne dai majalisar zantarwa ta amince da yi wa kasafin kudin kasar gyare-gyare, inda ta kasafta cewa za a kashe naira tiriliyan 10.5.

Sai dai da ta ke amincewa da kasafin, majalisar ta yi kari na naira biliyan 300 kan abinda majalisar zartarwa wadda shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta gabatar.

Majalisar ta amince da kasafin bayan da jagoran kwamitin kasafin kudi, Sanata Barau Jibrin, ya gabatar da rahoto, inda ta ce zai fara aiki da zarar shugaba Buhari ya bayar da tabbacin sa.

Buhari da Sanata Ahmed Lawan
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Buhari da Sanata Ahmed Lawan Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

A shawararta ta ranar da ta gabata, majalisar ta dakatar da yunkurin da ta ke na amincewa da kwaskwarimar da aka yi wa kasafin kudin na bana.

Hakan ya biyo kuskuren ɗab'i da aka samu a kwaskwarimar da aka yi wa kasafin kudin, yayin da sauye-sauyen bai hararo naira biliyan 186 da aka kasaftawa sashen kiwon lafiya na kasar ba.

Yayin da ya ke gabatar da kudirin, Sanata Jibrin ya ankarar da abokan aikinsa game da batun rage kasafin kudin sashen kiwon lafiya.

DUBA WANNAN: Dakarun ketare sun fi samun nasara a kan mayakan Boko Haram fiye da na Najeriya - NST

Sanata Barau ya ce fadar shugaban kasa ba ta hararo duk naira biliyan 500 na kudin tallafi da aka ware domin kula da lamarin annobar korona ba a sauyin da aka yi wa kasafin kudin na bana.

A yayin da ya hararo naira biliyan 314 a wani ɓangare cikin kudin tallafin, cikon naira biliyan 186 da aka ware wa fannin kiwon lafiyar bai nuna ba.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya nuna bacin rai game da yadda fadar shugaban kasa ta yi kurakurai na shigar da kasafin da za a jibinci reshen kiwon lafiya.

Ahmad Lawan ya ce da ace wanda nauyin tattaro bayanan kasafin kudin a hannunsu yake sun yi abinda ya dace, da wannan kuskure bai auku ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel