Kotu ta tabbatar da soke jam'iyyun siyasa 32 da Hukumar INEC ta yi

Kotu ta tabbatar da soke jam'iyyun siyasa 32 da Hukumar INEC ta yi

A ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da karar da ke kalubalantar kwace rajistar jam’iyyun siyasa 32 a Najeriya da Hukumar INEC ta yi.

Mai shari’a Anwuli Chikere shi ne ya yi watsi da karar da jam’iyyun suka shigar inda ya ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta na da ikon rusa su.

Alkalin ya yanke hukunci cewa, INEC ta na da cikakken 'yancin soke jam'iyyun bisa dogaro da tanadin sashe na 225 (a) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Jam’iyyun da ke kalubalantar hukuncin da INEC ta zartar na daga cikin jam'iyyu 74 da ta soke a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2020, saboda dalilan rashin yin kwazo a babban zaben na 2019.

Da yake bayyana dalilan yin watsi da jam’iyyun, shugaban INEC, Mahmood Yakubu ya ce jam’iyyun sun kasa cika ka’idojin da kundin tsarin mulki ya shata na ci gaba da wanzuwar jam’iyyun siyasa a Najeriya.

Shugaban Hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu
Shugaban Hukumar INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu
Asali: Original

INEC ta ce jam’iyyun da aka soke sun karya sharadin ci gaba da kasancewarsu yayin da suka gaza samun akalla kuri’u 2596 da aka jefa a koda jiha daya ta kasar yayin zaben shugaban kasa.

INEC ta kuma ce jam’iyyun, tun bayan kasancewar jam'iyyun, ba su taba yin nasara ba koda a karamar hukuma daya a duk fadin kasar a zaben gwamnonin jihohi.

A cewar INEC, cikin dukkanin jam'iyyun da ta kwace rajistarsu, babu jam'iyya daya da ta iya samun nasara a koda Unguwa daya yayin zabukan kananan hukumomi.

KARANTA KUMA: Dakarun ketare sun fi samun nasara a kan mayakan Boko Haram fiye da na Najeriya - NST

Haka kuma jam'iyyu ba su taba samun nasara ba a zaben 'yan majalisar dokokin jihohin ballantana kuma na majalisar tarayya.

Kamar yadda jaridar Guardian ta wallafa, a da can Najeriya tana da jam'iyyun siyasa 90 gabanin INEC ta kwace rajistar 74, inda adadinsu ya dawo 16 kacal.

Jam'iyyun siyasa 32 da suka nemi kotu ta share musu hawaye amma hakar su bata cimma ruwa ba sun hadar da;

  1. Advanced Congress of Democrats (ACD)
  2. Advanced Nigeria Democratic Party (ANDP)
  3. All Blending Party (ABP)
  4. All Grand Alliance Party (AGAP)
  5. Better Nigeria Progressive Party (BNPP)
  6. Democratic People’s Congress (DPC)
  7. Justice Party (FJP)
  8. Green Party of Nigeria (GPN)
  9. Mega Party of Nigeria (MPN)
  10. National Interest Party (NIP)
  11. Nigeria Democratic Congress Party (NDCP)
  12. People’s Party of Nigeria (PPN)
  13. People for Democratic Change (PDC)
  14. Peoples Coalition Party (PCP)
  15. Progressives Peoples Alliance (PPA)
  16. Red-build Nigeria Party (RBNP)
  17. Restoration Party of Nigeria (RP)
  18. United Democratic Party (UDP)
  19. United Patriot (UP)
  20. We The People Nigeria (WTPN)
  21. Young Democratic Party (YDP)
  22. Save Nigeria Congress (SNC)
  23. Change Advocacy Party (CAP)
  24. Socialist Party of Nigeria (SPN)
  25. All Grassroots Alliance (AGA)
  26. Alliance of Social Democrats (ASD)
  27. Democratic Alternative (DA)
  28. New Generation Party of Nigeria (NGP)
  29. Mass Action Joint Alliance (MAJA)
  30. Nigeria For Democracy (NFD)
  31. Masses Movement of Nigeria (MMN)
  32. Alliance for New Nigeria (ANN)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel