Dakarun ketare sun fi samun nasara a kan mayakan Boko Haram fiye da na Najeriya - NST

Dakarun ketare sun fi samun nasara a kan mayakan Boko Haram fiye da na Najeriya - NST

Dangane da kididdigar da Hukumar Kula da Al'amuran Tsaro ta Najeriya (NST) ta fitar, an kashe adadin masu tayar da kayar baya 1,596 a tsakanin 8 ga Afrilu zuwa 8 ga Yuni.

Wannan adadi ya yi kusa da kiyasin da Shugaban Hafsan Sojojin Kasan Najeriya, Lt. Janar Tukur Buratai ya ba da shaida bayan komawarsa fagen fama.

Buratai ya bayyana cewa, a tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni, dakarun sojin Najeriya sun kashe masu tayar da kayar baya 1,429.

Haka kuma ya ce an cafke mayakan Boko Haram, masu leken asiri da sauran masu ruwa da tsaki a sha'anin tayar da kayar baya 116 tun bayan komawarsa yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Furucin Shugaban Hafsan Sojin ya zo ne yayin ganawa da manema labarai a birnin Abuja, bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 8 ga watan Yuni.

Buhari da Buratai
Hakkin mallakar Hoto: Fadar shugaban kasa
Buhari da Buratai Hakkin mallakar Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

A ranar 8 ga watan Afrilun 2020, rundunar sojin kasar Chadi ta ba da sanarwa cewa ta kashe 'yan ta'adda dubu daya ta kuma tarwatsa jiragensu na ruwa guda hamsin.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin kakakin rundunar sojin kasa na kasar Chadi, Kanal Azem Bermendoa Agouna.

A wani simame da rundunar dakarun sojin kasar Kamaru ta kai tun a watan Mayu, ta samu nasarar kashe 'yan ta'adda biyar na kungiyar ISWAP, wani reshe na kungiyar Boko Haram.

A taikace dai, rundunar sojojin ta kashe kusan masu tayar da kayar baya 1,600 a tsakanin wannan lokaci.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Buhari ya yi ganawar sirri da mataimakinsa, Osinbajo

Alkaluma da dama sun nuna cewa, kashi 65.7 cikin dari na 'yan ta'addan da suka rasa rayukansu, na da alaka ne fafatawar da dakarun sojojin Chadi da na Kamaru suka yi amma ba na Najeriya ba.

Hakan na nuni da cewa, galibin nasarorin da aka samu a baya-bayan nan ba su da wata alaka da dakarun sojin Najeriya, sai dai sun ta'allaka ne da gumurzun dakarun kasar Chadi da na Kamaru.

A yayin ci gaba nazari kan alkaluman da NST ta fitar, yaƙe-yaƙen da dakarun sojin Najeriya suka yi ta janyo salwantar rayukan 'yan tawaye 591.

Babu shakka an samu ci gaba ta fuskantar nasarar da dakarun Najeriya suka samu a wannan lokaci idan an kwatanta da nasarar da suka samu a watannin biyu na baya.

A tsakanin watan Fabrairu zuwa Afrilu, rundunar sojin Najeriya ta kawar da masu tayar da kayar baya 509.

Sai dai kuma a tsakanin watan Dasumba na 2018 zuwa Fabrairun shekarar da muke ciki, masu tayar da kayar baya 620 sun yi gamo da karshensu a hannun masu kare martabar Najeriya.

Alkaluman NST sun nuna cewa, cikin watanni biyu da komawar Buratai yankin Arewa maso Gabas, sojoji 116 da farar hula 767 sun rasa rayukansu da suka hada da mutum 276 da suka fada tarkon masu garkuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel