Coronavirus: Buhari ya yi ganawar sirri da mataimakinsa, Osinbajo

Coronavirus: Buhari ya yi ganawar sirri da mataimakinsa, Osinbajo

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri tare da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni

- A yayin ganawar sun mayar da hankali kan yiwuwar bullo da manufofin da za su ba da damar farfado da tattalin arzikin Najeriya

- Babban makasudin zaman shi ne shimfida matakan mayar da annobar korona wata dama ta farfado da tattalin arzikin kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya shiga ganawar sirri tare da matamakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock a birnin Abuja.

Masu rike da madafan iko na kasar sun gana da juna a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni.

Ganawar ta gudana kwana guda kenan bayan da shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na hudu da aka kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

Buhari da mataimakinsa sun mayar da hankali kan yiwuwar bullo da manufofin da za su ba da damar farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Buhari da mataimakinsa, Osinbajo
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Buhari da mataimakinsa, Osinbajo Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Hakan yana kunshe cikin sakon da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya wallafa a kan shafinsa na Twitter.

Akande ya ce Buhari da mataimakinsa na da niyyar fito da wani tsari mai dorewa wanda za a iya bi wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Ya kuma bayyana cewa ganawar za ta duba yiwuwar aiwatar da wasu manufofin da za su taimaka wa gwamnatin tarayya ta mayar da cutar korona wata babbar dama ta habaka tattalin arziki, musamman a fannin samar da ayyukan yi.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Laraba shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a babban dakin taro na Council Chambers da ke fadarsa a Abuja.

KARANTA KUMA: Wata bakuwar cuta ta kashe shanu da dama a jihar Kano

Shi ne zaman majalisar na hudu da shugaban kasar ya jagoranta ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

An fara irin wannan zama wanda ya zama doka ta farko da aka fara bi tun a zaman majalisar na makonnin da suka gabata.

'Yan majalisar kalilan ne suka hallara a zauren da ake gudanar da taron, yayin da dama suke halartarsa ta hanyar bidiyo da aka hada da yanar gizo.

An zabi sauya salon zaman majalisar ne ta hanyar ba da tazara domin kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta da manufar dakile yaduwar cutar korona da ta zamto ruwan dare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel