Kashi 43% na talakawan duniya su na zaune a Indiya, Najeriya da Jamhuriyar Congo - Bankin Duniya

Kashi 43% na talakawan duniya su na zaune a Indiya, Najeriya da Jamhuriyar Congo - Bankin Duniya

Duk da ana tsammanin tattalin arzikin duniya zai habaka zuwa badi, amma har yanzu akwai mutanen da ke rayuwa cikin yanayi na kangin talauci.

A gargadin da Bankin Duniya ya yi a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, ya nuna cewa akwai yiwuwar wasu mutane da ke rayuwa cikin talauci za su dawwama a cikinsa.

Bankin Duniya ya yi wannan gargadi sakamakon mummunan tasirin da annobar cutar ta yi wa tattalin arzikin duniya baki daya.

Da wannan ne Bankin ya yi gargadin cewa, adadin mutanen da ke rayuwa cikin kangin na talauci ba zai sauya ba daga yanzu zuwa badi muddin annobar korona ba ta gushe ba.

Ya ce kasashe uku da ke da babban kaso na matalauta a duniya sun hadar da Indiya mai kashi 24%, Najeriya mai kashi 12% da kuma Jamhuriyar Congo mai kashi 7%.

Bankin Duniya ya ce wannan kasashe uku sun fi kowanne tara adadin mutane da talauci ya yi musu katutu a cikinsu saboda yawan al'umma da suke da su.

Kashi 43% na talakawan duniya suna zaune a Indiya, Najeriya da Jamhuriyar Congo - Bankin Duniya
Kashi 43% na talakawan duniya suna zaune a Indiya, Najeriya da Jamhuriyar Congo - Bankin Duniya
Asali: UGC

Haka kuma ya ce hasashe ya nuna cewa wannan mataki na talauci ba zai sauya ba a kasashen uku daga yanzu zuwa shekarar 2021.

An yi wannan hasashen yayin da wani Bankin bayar da rance a birnin Washington na kasar Amurka ya fidda kididdiga kan mummunan tasirin da annobar korona za ta haddasa a duniya.

KARANTA KUMA: Murnar zagayowar ranar haihuwa: Budurwa ta cakawa saurayinta wuka saboda ya aika mata da sakon text a madadin kiran salula

A kiyasin da Bankin ya fitar a ranar Litinin ya nuna cewa, annobar korona za ta jefa tsakanin mutum miliyan 70 zuwa miliyan 100 cikin matsanancin talauci a bana.

Kazalika kididdigar ta nuna cewa, matsin tattalin arziki da duniya za ta shiga ba a taba fuskantar makamacinsa ba tsawon shekaru 80 da suka gabata.

Gabanin barkewar annobar korona a duniya, an kayyade matsanancin talauci daga kan wadanda samunsu bai haura dala 1.90 a duk rana. Sai dai a yanzu lamarin yana kara tabarbarewa.

Da ya ke dai masu iya magana kan ce 'komai ya yi farko zai yi karshe', ana kyautata zaton tattalin arzikin duniya zai habaka da kashi 4 cikin dari a shekara mai zuwa.

Bankin ya kuma yi gargadin cewa, yankin Kudancin nahiyar Asiya, zai samu karin adadin matalauta sakamakon annobar korona, musamman a kasar Indiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel