Murnar zagayowar ranar haihuwa: Budurwa ta cakawa saurayinta wuka saboda ya aika mata da sakon text a madadin kiran salula

Murnar zagayowar ranar haihuwa: Budurwa ta cakawa saurayinta wuka saboda ya aika mata da sakon text a madadin kiran salula

A can kasar Birtaniya, an yankewa wata mata mai shekaru 46, hukuncin dauri na shekara shida a gidan kaso, bayan kama ta da laifin cakawa saurayinta, Alan Pearce, wuka.

Cikin rahoton da jaridar The Punch ta ruwaito, uwar 'ya'ya biyun ta aikata wannan mummunar ta'ada ne a ranar zagayowar haihuwarta.

Janet Kearns ta ce ta dabawa saurayin nata wuka saboda ya tura mata sakon text a madadin ya kira ta da wayar salulu domin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Ta ce zarginsa da ta ke na cewa ba ya rike amanar soyayyar da ke tsakaninsu ya sanya ta hau dokin zuciya wajen aikata wannan ta'addanci.

Murnar zagayowar ranar haihuwa: Budurwa ta cakawa saurayinta wuka saboda ya aika mata da sakon text a madadin kiran salula
Murnar zagayowar ranar haihuwa: Budurwa ta cakawa saurayinta wuka saboda ya aika mata da sakon text a madadin kiran salula
Asali: Facebook

Bayan dabawa Alan wuka a gidansa da ke Wythenshawe a birnin Manchester, Janet ta kama gabanta ba tare da ko waiwayen halin da ta bar shi a ciki walau zai yi rai ko sabanin haka.

A rahoton da shafin Dailymail.co.uk ya ruwaito, Janet ta garzaya har gidan Alan inda ta nemi jin dalilin da ya sanya bai kira ta da wayar salula ba sai dai sakon text kawai ya tura mata da shi.

Nan da nan ta dauki wuka mai tsawon inci shida ta daba masa, inda ya rika karaji da kururwar neman 'yan sanda su kawo masa dauki.

A gaggauce an garzaya da Alan asibiti inda aka yi masa tiyata ba shiri saboda raunin da ta gadar masa.

A gaban wata Kotu a birnin Manchester, Janet ta amsa laifinta da cewa ta aikata hakan ne da gayya.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Majalisar Wakilai ta kira Sadiya Umar kan rarraba kudin tallafin rage radadi

Yayin da ta ke zartar da hukunci, mai shari'a Hilary Manley, ta shaidawa Janet cewa, "kishin da ya mamaye dangartakar da ke tsakaninki da Mista Pearce, ta sanya kika kai masa hari."

"Kin yi amfani da wuka mai tsawon inci shida wajen gadar masa da rauni mai muni. Kin yi nufin yi masa mummunan lahani da gayya."

"Da wannan ne kotu ta zartar miki da hukuncin dauri na shekaru shida."

A rahoton da rundunar 'yan sandan ta gabatar a gaban kotu, ta bayyana cewa "an riski Alan ne kwance jina-jina ya na magagin mutuwa a cikin gidansa."

"Ba don jami'an agajin gaggawa sun yi hanzarin kai shi asibiti ba, da tuni wani labarin ake ji daban da na yanzu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel