Kwaskwarimar da aka yi wa kasafin kuɗin bana ba ta samu shiga ba a majalisar dattawa saboda kuskuren ɗab'i

Kwaskwarimar da aka yi wa kasafin kuɗin bana ba ta samu shiga ba a majalisar dattawa saboda kuskuren ɗab'i

Majalisar dattawa a ranar Talata ta dakatar da duba yiwuwar shigar da sauyin fasali da aka yi wa kasafin kudin kasar nan na bana cikin doka.

A yayin zamanta na ranar da ta gabata, majalisar ta jingine la'akarin da ta ke shirin yi na amincewa da sauye-sauyen da aka yi wa kasafin kudin kasar na bana.

Hakan ya biyo kuskuren ɗab'i da aka samu a kwaskwarimar da aka yi wa kasafin kudin, yayin da sauye-sauyen bai hararo naira biliyan 186 da aka warewa sashen kiwon lafiya na kasar ba.

Yayin da ya ke gabatar da kudirin, shugaban kwamitin Majalisar kan kasafi da tsare-tsare, Barau Jibrin, ya jawo hankalin abokan aikinsa game da batun cire kudaden a kasafin kudin da aka sauya wa fasali.

Zauren majalisar dattawan Najeriya
Zauren majalisar dattawan Najeriya
Asali: UGC

Lamarin da ya tilastawa majalisar ta jingine batun la'akari da kasafin N10.509trn da aka yi wa kwaskwarima da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar makonni biyu da suka gabata.

A ranar Talatar ne dai majalisar ta kudiri aniyar tattaunawa kan manyan ka'aidoji da kuma shawarwarin da aka sauya a kasafin kudin kasar wanda ta fara tun a makon da ya gabata.

KARANTA KUMA: Dokar cin-gashin-kan Majalisar jihohi da bangaren shari’a: Babu gudu babu ja da baya - Buhari

Sai dai a yanzu sanatocin ba su iya samun kwafin rahoton kwamitin kasafi na majalisar ba, saboda kuskuren da ofishin kasafi da ke karkashin fadar shugaban kasa ya tafka.

Sanata Barau ya ce ofishin kasafin kasar bai hararo dukkanin naira biliyan 500 na kudin tallafi da aka ware domin jibintar lamarin annobar korona ba a sauyin da aka yi wa kasafin kudin na bana.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

A yayin da ya hararo naira biliyan 314 a wani ɓangare cikin kudin tallafin, ragowar naira biliyan 186 da aka ware wa fannin kiwon lafiyar bai nuna ba.

Shugaban majalisar dattawan, Sanata Ahmed Lawan, ya ce da ace wadanda nauyin tattaro bayanan kasafin kudin a hannunsu yake sun yi abinda ya dace, da wannan kuskure bai auku ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel