Najeriya ta yi rashin shahararren dan kasuwar man fetur

Najeriya ta yi rashin shahararren dan kasuwar man fetur

- Babban dan kasuwar man fetur na Najeriya, Anthony Enukeme ya mutu sakamakon gajeriyar rashin lafiya

- Kafin rasuwar mamacin, ya cika shekaru 75 a duniya kuma ya cika shekaru 50 da yin aure a ranar 2 ga watan Mayu

- Majiya daga iyalansa ta ce, sakamakon hana zirga-zirga da aka yi saboda korona, dan kasuwar ya kasa samun damar duba lafiyarsa

Daya daga cikin manyan 'yan kasuwar man fetur din Najeriya, Anthony Enukeme ya rasu. Ya rasu yana da shekaru 75 a duniya.

Mamallakin kamfanin Tonimas Oil and gas group ya rasu a daren Litinin bayan gajeriyar rashin lafiya.

Wata majiya daga iyalansa wacce ta zanta da jaridar The Nation, ta ce ya mutu ne sakamakon hana zirga-zirgar da aka yi saboda annobar korona.

Ya ce mamacin ya cika shekaru 75 cif a duniya a watan Janairun da ta gabata. Ya saba fita kasar ketare don duba lafiyarsa a kowacce shekara amma sai wannan annobar ta hana.

Enukeme shine shugaban sarakunan gargajiya na jihar Anambra na tsawon lokaci.

Jajirtaccen mabiyin darikar katolika na addinin kiristar zai yi murnan cikarsu shekaru 50 da aure a ranar 2 ga watan Mayu amma wannan annobar ta hana.

Najeriya ta yi rashin shahararren dan kasuwar man fetur
Najeriya ta yi rashin shahararren dan kasuwar man fetur. Hoto daga The Nation
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, Jadegoke Adebonajo Badejo babban lauyan Najeriya ne wanda ya yanke jiki ya fadi a yayin da yake fita daga gidansa a ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni.

Badejo shine babban mai hannun jari a Bonajo Badejo & Co, ya rasu yana da shekaru 61 a duniya, jaridar The Nation ta ruwaito.

"Ya shirya tsaf don fita daga gida. Yana kokarin fita aiki ne a jiya da ya yanke jiki ya fadi kuma ya mutu a take," in ji wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta.

Ya kammala digirinsa na farko a jami'ar Ife wacce a yanzu ake kira da jami'ar Obafemi Awolowo da kuma digirinsa na biyu a jami'ar jihar Legas.

A dayan bangaren, Alfred Oghogho Eghobamien ya rasu a ranar Juma'a yana da shekaru 85. Eghobamien mahaifi ne ga Osaro Eghobamien wanda shi ma babban lauya ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel