'Yan sanda sun kama mata biyu da ake zargi da satar kananan yara

'Yan sanda sun kama mata biyu da ake zargi da satar kananan yara

Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta damke wata mata mai shekaru 28 mai suna Victoria Joseph da wata mai shekaru 33 mai suna Joy Ugorji a kan zarginsu da ake da satar yaro mai shekaru 2 daga jihar Ribas.

A yayin damke wadanda ake zargin a ranar Talata, kwamishinan 'yan sandan jihar Imo, Isaac Akinmoyede ya ce sun sato yaron ne daga Kakuano da ke jihar Ribas inda suka zo siyar da shi a Imo.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce an damke wadanda ake zargin tare da ceto yaron, jaridar The Nation ta wallafa.

Ya ce, "A ranar 30 ga watan Mayun 2020, yayin duba motoci masu wuce, jami'ai sun ceto wani yaro mai kimanin shekaru biyu daga hannun wasu mata biyu.

"Bayan tuhumarsu, sun tabbatar da cewa sato yaron suka yi daga Kakuano da ke jihar Ribas sannan suka kai shi Imo don siyarwa.

"An mika yaron gidan marayu yayin da ake kokarin gano iyayensa.

"A don haka rundunar ke kira ga duk wanda dan sa ya bace ko ya san wanda dan sa ya bace da ya hanzarta kiran lambar 'yan sandan."

Joseph ta sanar da manema labarai cewa ta sato yaron ne daga wurin kakarsa.

Ta ce mahaifiyar yaron 'yar uwarta ce kuma ta yi amfani da sanayya ne wurin sace shi.

Wacce ake zargin ta ce abokan barnarta na jihar Imo don su ke nemo mata masu siya.

Ta tabbatar da cewa ta taba siyar da wasu yaran a baya.

'Yan sanda sun kama mata biyu da ake zargi da satar kananan yara
'Yan sanda sun kama mata biyu da ake zargi da satar kananan yara. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta

A wani labari na daban, likitoci a kasar India sun sha mamaki bayan da suka cire cajar waya mai tsawon kafa biyu daga mafitsarar wani mutum mai shekaru 30 bayan fara bude cikinsa da suka yi.

Majinyacin wanda a halin yanzu ake bincikar lafiyar kwakwalwarsa, ya sanar da likitocin cewa ya hadiye cajar ne ta bakinsa amma sai suka gano cewa ta mazakutarsa ta shiga.

Daya daga cikin likitocin da ya yi wa mutumin aiki, Wallie Islam ne ya wallafa labarin a Facebook. Ya ce majinyacin ya dinga korafin ciwon ciki sannan akwai lokacin da ya hadiye amsa kuwwar waya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel