Sojoji sun ci gaba da yi wa mayakan Boko Haram kisan kare dangi a Arewa maso Gabas

Sojoji sun ci gaba da yi wa mayakan Boko Haram kisan kare dangi a Arewa maso Gabas

A yayin ci gaba da tsananta ayyukan kakkabe ta'addanci a yankin Arewa maso Gabas, 'yan Boko Haram sun ci gaba da mika wuya yayin da Sojoji ke musu kisan kare dangi.

Da safiyar ranar 8 ga watan Yuni, bataliyar soji da ke kula da yankin Gwoza a jihar Borno, ta kai wani simame maboyar mayakan Boko Haram da ke kan tsaunukan Mandara a Kwatara.

Hukumar dakarun sojin kasan Najeriya ce ta bayyana hakan cikin sanarwar da ta wallafa a wani sako kan shafinta na Facebook a ranar Talata, 9 ga watan Yuni.

Gwarazan dakarun cikin hikima sun hau saman tsaunin inda suka yi wa 'yan ta'addan kawanya ruwan wuta inda da yawansu suka kwanta dama yayin da dama suka tsere da raunuka na harbin bindiga.

Haka kuma a wannan rana, bataliyar soji mai kula da yankin Miyanti, ta yi wa mayakan Boko Haram shigar ba zata a kan hanyar Darel Jamel zuwa Miyanti.

Mayaka 2 na kungiyar masu tayar da kayar baya sun kwanta dama yayin da dakaru suka ceto wasu mata biyu. Sun kuma tsinto kekuna biyu, buhu guda cike da takalmin Silipa da kuma tsabar kudi har Naira 25,500.

Yayin horas da dakarun sojin kasa kan sarrafa tankar yaki
Hakkin mallakar Hoto: Defense News Nigeria
Yayin horas da dakarun sojin kasa kan sarrafa tankar yaki Hakkin mallakar Hoto: Defense News Nigeria
Asali: Twitter

A wannan hari da bataliyar soji mai kula da yankin Gamboru ta kai, wani dan Boko Haram mai suna, Mustapha Kori ya mika wuyansa.

Dan ta'addan ya ce ya shafe tsawon shekaru biyar a kan wannan harka ta tayar da kayar baya, kuma ya samu damar tserowa daga sansaninsu da ke yankin Fulatari a gabar takfin Chadi.

Ya bayyana nadamarsa da cewa wutar da dakaru ke hurowa a baya-bayan nan ta salwantar da rayukan da dama daga cikin abokan aikinsa da suka hadar har da wani kwamandansu.

A ranar 5 ga watan Yuni, bataliyar sojin da ke aikin kakkabe yankin Zabarmari a jihar Borno, yayin tsefe garuruwan Jajeri, Gurnum Kore I, Gurnum Kore II, Malis, da Ladin Mbuta yayin gudanar da sintiri.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Yadda za a nemi rancen N50bn da babban bankin Najeriya ya ware

Kazalika, dakarun sun tsefe yankunan Asala Fura, Mai Njika, Kanube, Kessa Ngala, Taula, da Shuwabe.

A garin Taula, dakari sun yi kicibus da maboyar mayakan Boko Haram, inda nan da nan 'yan ta'addan suka arce babu shiri. Sai dai uku da cikin su sun yi gamo da ajali a hannun dakarun.

Baya ga haka, a ranar 5 ga watan Yuni, bataliyar sojin mai sintiri a yankin Dusuman zuwa Zabarmari, ta samu nasarar yi wa 'yan Boko Haram shigar ba zata a wani simame da ta kai cikin dare.

Ta kawar da dan ta'adda guda daya, yayin da dama suka arce da raunuka na harbin bindiga. Ta kuma tsinto makaman yaki da dama da suka hadar da bindigu kirar Ak-47 da alburusai.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

A dai wannan rana, bataliyar soji da ke tsefe yankin Michika a jihar Adamawa, bayan samun wasu bayanai na sirri, ta samu nasarar cafke wani dan Boko Haram mai suna Kawalu ana cikin sallar Juma'a a babban masallacin Juma'a na Michika.

Bayan ya shiga hannu, Kawalu ya ce ya fito ne daga maboyar 'yan Boko Haram a sansaninsu na Maikadiri.

Shugaban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, yana ci gaba da yabawa kwazon sojojin musamman juriyar su, jarunta da kuma jajircewa wajen kare mutuncin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel