Coronavirus: Yadda za a nemi rancen N50bn da babban bankin Najeriya ya ware

Coronavirus: Yadda za a nemi rancen N50bn da babban bankin Najeriya ya ware

A kokarin rage radadi da tasirin matsin tattalin arziki da annobar korona ta haddasa, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gabatar da wani shirin karfafawa 'yan Najeriya.

Babban shirin tallafin shi ne CBN ta ware Naira biliyan 50 domin bayar da rance ga magidanta, da masu kanana da manyan masana'antu wanda annobar korona ta jefa cikin rauni.

Gwamnan babban bankin Najeriya; Godwin Emefiele tare da shugaba Muhammadu Buhari
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Gwamnan babban bankin Najeriya; Godwin Emefiele tare da shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Ga jerin rukunan wadanda babban bankin ya yi wa tanadin rancen kamar haka:

1. Magidanta:

Magidanta 'yan Najeriya masu harkar yi. Amma sai sun gabatar da cikakkiyar shaidar yadda annobar korona ta yi wa rayuwarsu mummunan tasiri.

2. Masu 'yar karamar sana'a:

Masu 'yan kananan sana'o'i wanda suke da cikakkiyar shaidar yadda annobar korona ta jefa harkokin kasuwancinsu cikin rauni.

3. Kananan masana'antu:

Masu kananan masana'antu wadanda suke da tsare-tsaren samun damar cin duk wata moriya da za ta taso saboda annobar korona.

Legit.ng za ta zame muku jagora a kan hanyoyin da za ku bibiya ta yadda zaku iya neman rancen idan kun kasance a karkashin rukunan wadanda suka cancanta.

KARANTA KUMA: Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda luguden wuta a Zamfara

Mataki na farko: Shigar da bukatar nema

Shigar da bukatar neman rancen shi ne mataki na farko. Ya ake yin wannan? Wannan abu ne mai sauki.

Ana shigar da bukatar ne ta hanya wayar salulua ko kwamfuta ko kuma duk wata na'urar sadarwa mai amfani da fasahar zamani.

Ana gabatar da bukatar neman rancen ne kai tsaye a shafin bankin raya masana'antu na NIRSAL Microfinance Bank (NMFB). Ga shafin yanar gizon kamar haka: nmfb.com.ng/covid-19-support/.

An yi sa'a babban bankin na Najeriya ya dauke bukatar gabatar da wanda zai tsayawa masu karbar rancen a matsayin jingina.

CBN ya ba da tabbacin wannan dalili da cewa, ya dauke bukatar gabatar da wanda zai tsaya a matsayin jingina domin saukakawa manema rancen kudin.

Mataki na biyu: Amincewa

A mataki na biyu bankin NMFB zai yi nazari da kuma bayyana yardarsa a kan bukatar neman rancen kudin da aka shigar, sannan ya mika wa babban bankin bukatar wanda shi ne zai ba da amincewa ta karshe.

Mataki na uku: Fitar da kudi

Da zarar babban bankin ya kammala nazari da bita kan cancantar bukatar da aka shigar ta neman rancen kudin a matakin karshe, zai kuma yarjewar bankin NMFB raba kudaden ga mabukatan.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

CBN ya bayar da tabbacin cewa, duk wadanda cancanta kuma suka samu nasarar cika sharudan da aka shata ta basu rancen, za su samu kudaden cikin awanni 48.

Ga wadanda kuma suka shigar da bukatar amma har yanzu shiru basu samu kudaden da suka nemi rance ba, CBN ya shawarce su da su ziyarci shafin bankin NMFB (www.nmfb.com.ng) domin sabunta bayanan asusunsu na ajiya.

Ga masu korafi:

Ga duk wani mai korafi, ana iya kiran lambar wayoyi kamar haka: 09010026900, 09010026900. Ko kuma a aika sakon e-mail zuwa covid19@nmfb.com.ng

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel