Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda luguden wuta a Zamfara

Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda luguden wuta a Zamfara

A ranakun 2 da 3 ga watan Yuni, 'yan ta'adda suka mamaye garuruwan Maru da Mafara, inda suka kashe sama da mutum 70 kamar yadda kafar watsa labarai ta Human Angle ta ba da rahoto.

Dakarun soji sun mayar da martanin wannan hari kan masu tayar da kayar da bayan ta hanyar barin wuta daga sama inda suka kashe 'yan ta'adda da dama.

Sojoji sun kai wannan hari na bazata a ranar 7 ga watan Yuni, kamar yadda babban jami'in gudanar na hukumar dakarun sojin kasa, Manjo Janar John Eneche, ya sanar.

Wani kasurgumin dan ta'adda da ya yi kaurin suna, Dogo Gide, yana daga cikin wadanda harin dakarun sojin ya ritsa da su.

An ruwaito cewa, Dogon Gide ya samu rauni inda a halin yanzu yana can yana fama da jinya.

Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda luguden wuta a Zamfara
Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda luguden wuta a Zamfara
Asali: Facebook

A barin wutar da dakarun sojin suka yi, sun yi fata-fata da maboyar wasu kungiyoyin 'yan ta'adda har kashi uku.

Kuma wannan harin na bazata da sai dai kawai barin wuta suka ji daga sama, ya gadar musu da asara mai girman gaske kamar yadda mashaida suka bayar da rahoto.

Mafi shahara cikin masu tayar da kayar bayan shi ne, Dogo Gide, wanda ya fito daga reshen kungiyar 'yan ta'adda ta Ansaru, wadda ake zargi tana da nasaba da kungiyar Al-Qaeda.

KARANTA KUMA: Obasanjo ya yi kashedi game da matsalar karancin abinci da za a fuskanta bayan annobar korona ta gushe

Sai dai an ruwaito cewa, Gide ya kasance yana yaki da wasu kungiyoyi na masu tayar da kayar baya da suka ki yin sulhun da wasu gwamnonin jihohi a yankin Arewa maso Yamma suka nema.

Majiyoyin rahoto sun bayyana cewa, kasancewar Gide a yankin da sojoji suka kai hari abu ne mai ban mamaki saboda ba a saba da shi ba kuma akwai damuwa a tattare da wannan lamari.

Sun ce ta yiwu Gide ya kasance a wurin ne yayin fafutikarsa ta neman kulla hadin gwiwa da wasu kungiyoyin na masu tayar kayar baya domin tunkarar dakarun soji.

Kamar yadda Human Angle ta ruwaito a watan da ya gabata, kungiyoyin masu tayar da kayar baya sun gana da juna domin kulla yarjejeniyar hadin kai da manufar zama ayari guda.

Kungiyoyin sun nemi ajiye banbancinsu a gefe domin ci gaba da ta'azzarar al'umma da kuma yakar dakarun soji a matsayin madauri daya.

Sai dai a yanzu da azal ta afka masa, Gide da wasu kwamandu biyu a yankin Dandalla da ke jihar Zamfara, na ci gaba fama da jinya ta raunin da harin dakarun soji ya gadar musu.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, harin da dakarun soji suka kai ya yi babbar barna a maboyar masu tayar da kayar baya ta Dandalla, Bingi da Yan-Bana da ke yankin Kuyanbana.

Majiyar wadda ta fito daga dakarun sojin ta bayyana cewa, dajin Kuyanbana yana bai wa masu tayar da kayar baya mafaka saboda yanayin na tsananin duhun ciyayi da tsirrai.

A yayin tattara wannan rahoto, ba a iya sanin girman raunin da harin dakarun sojin ya gadar wa Dogo Gide ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel