Bidiyon tsotse gaban jariri: 'Yan sanda na neman budurwa ido rufe

Bidiyon tsotse gaban jariri: 'Yan sanda na neman budurwa ido rufe

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bada umarnin damko wata budurwar da ke wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani. A bidiyon, an ga budurwar na tsotsar gaban yaro jinjiri.

A bidiyon mai tsawon sakanni 29, an ga matar ta dukar da kanta kasa tana tsotse gaban yaron.

Inda aka nadi bidiyon da kuma ranar da abun ya faru har yau ba a gano ba. Ba a kuma san ko mahaifiyar yaron ta san abinda ya faru ba, jarida The Cable ta wallafa.

Wannan al'amarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani inda mutane da yawa ke kira ga hukumomin da suka dace don daukar matakin da ya dace.

Amma wata wallafa da rundunar 'yan sanda ta yi a shafinta na twitter, ta yi kira ga jama'a da su taimaka da duk wani bayani da ya danganci matar.

Ta tabbatar da cewa za a boye suna da duk wani abu da zai bayyana matar.

"Duk wanda ke da bayani kamar: suna, lambar waya, adireshi na matar da ke wannan hoton, a tura mana ko a kira mu. Muna bada tabbacin boye bayanan duk wanda ya sanar mana," suka wallafa.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, dan majalisar wakilai, Ahmed Jaha dan asalin jam'iyyar APC daga jihar Borno, ya ce ya yi nadamar gatsalin da ya yi wa mata a kan fyade a majalisar yayin da ake tafka muhawara a ranar Alhamis.

Ya nemi yafiyar 'yan Najeriya, ballantana mata.

A wata tattaunawa da Jaha ya yi da manema labarai a ranar Asabar a Abuja, ya tuna da tsokacin da ya yi ga mata a zauren majalisa inda ya bukacesu da su koyi dabi'ar shigar mutunci don gujewa fyade ko cin zarafi daga mazan da basu iya saisaita kansu.

A makonni da suka gabata, 'yan Najeriya na ta magana a kan yadda al'amarin fyade ya yawaita tare da cin zarafin kananan yara.

A kalla mata biyu aka kashe a makonni da suka gabata bayan an yi musu fyade, lamarin da har yanzu 'yan sanda ke bincika.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Chibok, Damboa da Gwoza a tarayya, ya ce ya yi nadamar wannan maganar da yayi don ta matukar tunzura mata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel