Takunkumin rufe fuska kadai ba ya hana kamuwa da cutar korona - WHO

Takunkumin rufe fuska kadai ba ya hana kamuwa da cutar korona - WHO

- Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta fitar da sabbin ka'idoji game da yadda ya dace a rika amfani da takunkumin rufe fuska domin dakile yaduwar cutar korona

- A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar cutar korona, an yaba da yadda takunkumin rufe fuska ya kasance daya daga cikin ababen kariya na kamuwa da cutar

- Sai dai yanzu wani sabon bincike ya nuna cewa, takunkumin rufe fuskar shi kadai ba ya da ingancin hana kamuwa da cutar har sai an kiyaye wasu ka'idoji na kare kai

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta shata wasu sabbin sharadi na yin amfani da takunkumin rufe fuska a yayin da likafar annobar cutar korona ke ci gaba babu sassauci.

A karshen makon da ya gabata hukumar ta bayyana cewa, sanya takunkumin rufe fuska kadai ba ya da cikakkiyar nagarta ta hana kamuwa da kwayoyin cutar mai sarkafe kafofin numfashi.

A halin yanzu, akwai kimanin mutum miliyan 6.8 da cutar ta harba a fadin duniya, yayin da tuni mutum 397,388 suka riga mu gidan gaskiya. An samu fiye da mutum miliyan 3.3 da suka warke.

Da ya ke jawabi a taron manema labarai a birnin Geneva na kasar Switzerkand, shugaban Hukumar WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi karin haske kan amfani da takunkumin rufe fuska.

Shugaban Hukumar WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus
Asali: UGC

Adhanom ya ce, ya kamata mutane su rika amfani da takunkumin rufe fuska tare da kiyaye sauran matakai da ka'idodin kare kai na kamuwa da cutar korona.

Sauran matakan da ya kamata a dabi'antu da su ba ya ga sanya takunkumin rufe fuska su ne tsaftace hannaye akai-akai da kuma kiyaye dokar nesa-nesa da juna tare da bayar da tazara.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Dalibai sun koma aji a Afrika ta Kudu

Ya ce,"a yankunan da ake samun yaduwar cutar, ana shawartar mutanen da suka haura shekaru 40 kuma suke fama da wasu cututtukan na daban, da su rika sanya takunkumin rufe fuska yayin da aka gaza kiyaye dokar nesa-nesa da juna."

Tedros ya ce "rashin amfanin da takunkumin rufe fuska ta yadda mahukuntan lafiya suka shar'anta, zai jefa mutane cikin hadarin kamuwa da cutar."

"Mutane za su iya shafa wa kawunansu cutar idan suka yi amfani da hannayen da ba a tsaftace su ba wajen gyara zaman takunkumin da suka rufe fuskokinsu da shi."

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

"Ko kuma wajen cire wa da mayar da takunkumin rufe fuskar da hannayen da ba su da tsafta."

"Babu shakka takunkumin rufe fuska yana da fa'ida a matsayin wani ɓangare na ingantacciyar hanya ta yaƙi da cutar korona, saboda a fakaice yana kawar da tsoro da tunanin kamuwa da cutar."

"Ban san ta ya zan fada a fahimta ba, amma takunkumin rufe fuska shi kadai ba zai kare mutum daga kamuwa da cutar korona ba," inji Tedros.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel