Coronavirus: Dalibai sun koma aji a Afrika ta Kudu

Coronavirus: Dalibai sun koma aji a Afrika ta Kudu

A yanzu haka dai kasashen duniya da dama na ci gaba da sassauta dokar kullen da suka shimfida sanadiyar annobar korona da ta bulla a watannin baya.

Mun samu cewa, bayan da gwamnati ta sassauta dokar kulle a kasar Afirka ta Kudu, an ci gaba da buɗe makarantu a kasar yayin da makarantun suka cimma duk ka'idodin da aka shata musu na buɗewa.

Ma'aikatar ilimin kasar ta ce kashi 95 cikin 100 na makarantun sun cimma duk ka'idodin da aka sanya musu na buɗewa, inda a yanzu galibin dalibai sun koma aji wajen daukan darussa.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, dalibai a Afrika ta Kudu sun koma aji bayan da gwamnati ta yi feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka a harabar makarantun kasar.

Bayan dage komawa makarantun da mako daya domin daukar matakan da suka dace, haka kuma gwamnatin kasar ta samar da takunkunman rufe fuska da rigunan kariya domin dakile yaduwar cutar korona.

Kafofin sadarwa da sun yada rahotanni cikin bidiyo na yada dalibai suka koma aji tare da nuna yadda suke daukar darasi yayin komawarsu a ranar Litinin.

KARANTA KUMA: Daraktoci 50 sun faɗi jarrabawar ɗaga likafarsu zuwa matakin sakatarorin dindindin - Yemi Esan

A halin yanzu shugabannin makarantu na ci gaba da aiki tukuru wajen ganin dalibai sun kiyaye dokar nesa-nesa da juna da bayar da tazara a tsakaninsu kamar yadda aka gindaya.

Haka kuma mahukunta na ci gaba da dagewa wajen tabbatar da dalibai sun wanke hannayensu da sabulu a karkashin ruwa mai gudana ko kuma sunadarin wanke hannu (sanitzer).

Ana kuma gwada zafin jikin dalibai yayin da suka isa makaranta domin tantance koshin lafiyarsu.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Ministar ilimin kasar, Angie Motshekga, ta ce su na ci gaba da ba da himma ta hadin gwiwa da makarantun da ba su bude sakamakon fuskantar kalubalen tsaftace harabarsu.

Haka kuma ta bayyana irin lalata makarantun da aka yi a lokacin da suke rufe a matsayin wani kalubale da suke fuskanta.

A yayin jaddada cewa babu makarantar da za a bari ta ci gaba da harkokin karantarwa ba tare da ta kiyaye matakan kariya da aka shata ba, sai dai ta ce babu dalibin da za a bari a baya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel