Daraktoci 50 sun faɗi jarrabawar ɗaga likafarsu zuwa matakin sakatarorin dindindin - Yemi Esan

Daraktoci 50 sun faɗi jarrabawar ɗaga likafarsu zuwa matakin sakatarorin dindindin - Yemi Esan

Gwamnatin Tarayya ta fitar da jerin Daraktoci 41 da suka samu nasarar wucewa zagayen karshe na jarabawar ɗaga likafarsu zuwa matakin sakatarorin dindindin.

Darakatocin 41 sun fito ne daga cikin mutum 91 da suka zana jarabawar tantance ƙwarewarsu ta Fasahar Sadarwar Zamani a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

Wannan ya nuna cewa manyan ma'aikatan gwamnati 50 da suka zana jarabawar ba su yi nasara ba kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Manema labarai a ranar Asabar sun samu kwafin wasikar da ta bayyana jerin manyan ma'aikatan 41 da suka samu nasarar wucewa zagayen karshe na jarabawar ɗaga likafarsu.

Wasikar tana dauke da kwanan watan ranar 6 ga Yunin 2020 wadda darekan ofishin kula da sakatarorin dindidin, I.A Mairiga, ya sanya wa hannu a madadin shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan.

Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan.
Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan.
Asali: Twitter

Mairiga ya lura cewa, a yanzu Daraktoci 41 da suka samu nasara za su zauna zagayen karshen na jarabawar ɗaga likafarsu, wadda za ta kasance zantawar baki, a ranar Litinin, 8 ga watan Yuni.

A wasikar mai lamba HCSF/CMO/AOD/012/VOL. VI/42, ana gayyatar Daraktocin 41 su hallara a dakin taro na Olesugun Obasanjo da ke harabar Sakateriyar Tarayya da misalin karfe 8.00 na safiyar Litinin.

KARANTA KUMA: Covid-19: Hukumar WAEC ta fadi lokacin zana jarabawar bana a Najeriya

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, 16 daga cikin Daraktocin 41 ne kadai ake sa ran za su zama sakatarorin dindindin kamar yadda wasikar ta bayyana.

Tun a sanawar da Yemi-Esan ta gabatar a ranar 23 ga watan Maris, ta nuna cewa za a gudanar da jarrabawar nada sabbin sakatarorin dindindin 16 a wasu ma'aikatu na gwamnatin tarayya.

Ta ce Daraktocin 14 da suka yi nasara za su maye gurbin sakatarorin dindindin da za su yi ritaya a bana, yayin da sauran biyun kuma za su maye guraben da babu kowa a kujerunsu.

Cikin sanarwar, sakatarorin dindindin da za su yi ritaya a bana sun fito ne daga jihohin Kebbi, Kwara, Abia, Anambra, Cross River, Kaduna, Kano, Oyo, Rivers, Sokoto, Adamawa, Yobe, Gombe da Jigawa.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Zamfara da Kogi su ne sauran jihohin biyu da ba su da sakatororin dindindin a kowane daya daga cikin ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Yemi-Esan ta sake nanata cewa, ɗaga likafar za ta takaita ne kadai a kan ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka kai matsayin darakta a matakin albashi na 17 kafin 1 ga watan Janairun 2018.

Haka kuma zana jarabawar ɗaga likafar za ta kasance kan ma'aikatan da suka sabunta bayanan su a kan tsarin biyan albashin bai-daya (IPPIS) da gwamnatin tarayyar kasar ta fito da shi .

Ta kara da cewa domin cancanta, irin wadannan jami'ai dole ne su fito daga wasu jihohin kasar nan kuma bai kamata su yi ritaya ba daga yanzu zuwa ranar 31 ga watan Dasumba na 2021.

Jihohin sun hada da Abia, Adamawa, Anambra, Cross River, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Kogi, Kwara, Oyo, Ribas, Sakkwato, Yobe da kuma Zamfara.

Karo karshe da aka nada sakatarorin dindindin shi ne a watan Dasumba na shekarar 2019 yayin da Gwamnatin Tarayya ta amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda tara.

Sakatarorin dindindin da aka nada a wancan lokaci sun hadar da:

Musa Hassan daga Jihar Borno;

Ahmed Aliyu daga Jihar Neja;

Olushola Idowu daga Jihar Ogun;

Andrew Adejoh daga Yakin Arewa Ta Tsakiya;

Umar Tijjani, daga Yakin Arewa maso Gabas;

Nasir Gwarzo, daga Yakin Arewa maso Yamma;

Nebeolisa Anako, mai wakiltar Yankin Kudu maso Gabas;

Fashedemi Peter, mai wakiltar Yankin Kudu maso Yamma;

Evelyn Ngige, mai wakiltar Yankin Kudu maos Kudu na Najeriya.

An nada sakatarori tara na dindindin daga cikin daraktoci 48 da suka halarci zagayen karshe na jarabawar ɗaga likafar aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel