NAPTIP ta fitar da sunayen masu cin zarafin mata a Najeriya

NAPTIP ta fitar da sunayen masu cin zarafin mata a Najeriya

- Yaki da cin zarafin bil adama ya ci gaba da kasancewa abu mai muhimmanci ga gwamnatin Najeriya

- Domin yin wannan a bayyane, Hukumar Kula da Fataucin Mutane (NAPTIP) ta fitar da cikakken jerin masu aikata laifin fyade a kasar

- NAPTIP ta ce ba za ta daina wallafa sunayen mutane da ke da hannu a aikata laifin ba

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tumke damarar da ba za ta gushe ba wajen ci gaba da yaki da cin zarafin mata ta hanyar lalata wanda ya ke neman zama ruwan dare a kasar.

Dame Julie Onak-Donli, shugaban Hukumar Yaki da Fataucin Mutane NAPTIP, ta wallafa jerin sunayen duk mutanen da aka yanke wa hukunci bayan kama su da laifin cin zarafi a fadin kasar.

Legit.ng ta fahimci cewa, Julie ta wallafa cikakken jerin sunayen masu wannan mummunan laifi a kan shafinta na Twitter a ranar Asabar, 6 ga watan Yuni.

Ta kuma ce za a ci gaba da wallafa sunaye gami da hotunan duk miyagun mutanen da aka zartarwa hukunci sakamakon kama su da laifin cin zarafin mata ta hanyar fyade.

Shugabar ta Hukumar NAPTIP ta ce galibin wadanda suke aikata wannan aika aikar na aiwatar da ita ne a sirrance kuma akasari su kan sha ba tare da an gano su ba.

KARANTA KUMA: Bayan shekaru shida da rasuwar Sarki Ado Bayero, an yi taron addu'a a fadar masarautar Kano

Shugabar hukumar yaki da safarar mutane NAPTIP Julie Okah-Donli ta ce, ''Rijistar masu aikata fyade na kunshe da sunaye da bayanan wadanda aka samu da aikata laifukan, da hotunansu, da shekaru, da garin da suke da duk muhimman bayanan da suka shafesu.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, ''Rijistar masu aikata fyade na kunshe da sunaye da bayanan wadanda aka samu da aikata laifukan, da hotunansu, da shekaru, da garin da suke da duk muhimman bayanan da suka shafesu."

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Hakan ya fito ne daga bakin Shugabar NAPTIP tun a watan Nuwamban 2019, yayin kaddamar da yin rajista ga mutanen da aka samu da laifin duk wani dangi na cin zarafin mata.

Tana mai cewa, "al'umma za su iya ganin dukkan bayanan wadanda aka yi wa rajistar, sannan za a iya ganin sunaye da hotunan wadanda ake bincike a kansu amma sai an biya wasu kudade kafin a ga jerin sunayen."

Manufar hakan kamar yadda Mrs Julie ta bayyana ta ce domin mutane su iya tantance abokanan da za su yi hulda da su a kowane irin sha'ani na rayuwar yau da kullum.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel