Yanzu-yanzu: Mutum 389 sun sake harbuwa da korona, jimilla 12233

Yanzu-yanzu: Mutum 389 sun sake harbuwa da korona, jimilla 12233

Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cutuka masu yaduwa (NCDC) ta bayyana a yau 6 ga watan Yunin 2020, an samu sabbin masu cutar korona 389 a Najeriya.

A jihar Legas an samu karin mutum 66 da ke dauke da muguwar cutar, yayin da babban birnin tarayya na Abuja ke biye da sabbin mutum 50.

Jihar Delta na da karin mutum 32, jihar Oyo ta samu karin mutum 31 sai kuma jihar Borno da ke yankin arewa maso gabas na kasar nan da ya samu karin mutum 26.

Jihar Ribas ta samu karin mutum 24, jihar Edo na da karin mutum 23, jihar Ebonyi na da karin mutum 23 sai kuma jihar Anambra da ke da karin mutum 17.

A jihar Gombe, an samu karin mutum 17, jihar Nasarawa akwai karin mutum 14, jihohin Imo, Kano da Sokoto na da karin mutum goma sha bibbiyu.

A jihar Jigawa akwai karin mutum 8, jihar Ogun an samu karin mutum 7 sai jihar Bauchi da ta samu karin mutum biyar.

Jihohin Kaduna, Kebbi da Katsina suna da karin mutum bibbiyu yayin da jihohin Abia da Niger suka samu kari mutum daddaya.

Jimillar masu cutar a Najeriya sun kai mutum 12,233, yayin da mutum 3826 suka warke daga jinyar cutar.

Mutum 342 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon annobar da ta zagaye duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel