NUC ta fitar da sunayen jami'o'in da aka ba lamunin gudanar da karatun gaba da digiri

NUC ta fitar da sunayen jami'o'in da aka ba lamunin gudanar da karatun gaba da digiri

A yanzu haka Najeriya ta na da jami'o'i 170. Guda 43 daga cikinsu na gwamnatin tarayya ne, yayin da 48 suka kasance na gwamnatin jiha sai kuma 79 da masu zaman kansu suka mallaka.

A cikin wata sanarwa da Hukumar kula da Jami'o'i a Najeriya (NUC) ta fitar a ranar 24 ga watan Maris, ta bayyana sunayen jami'o'in kasar nan da aka ba izinin gudanar da karatun digiri na gaba.

Sakamakon yaduwar mayaudaran jami'o'i a Najeriya masu ba da shaidar karatu na bogi, NUC ta gargadi jama'a kan wasu jami'o'i da ke gudanar da karatuttukan digiri na gaba ba tare da izini ba.

NUC ta fitar da sunayen jami'o'in da aka ba lamunin gudanar da karatun gaba da digiri
NUC ta fitar da sunayen jami'o'in da aka ba lamunin gudanar da karatun gaba da digiri
Asali: Depositphotos

Ga jerin Jami'o'in Gwamnatin Tarayya da aka bai wa lasisin karatun digiri na gaba a Najeriya:

1. Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi

2. Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria

3. Jami'ar Bayero, Kano

4. Jami'ar Tarayya ta Fasaha, Akure

5. Jami'ar Tarayya ta Fasaha, Minna

6. Jami'ar Tarayya ta Fasaha, Owerri

7. Jami'ar Micheal Okpara ta Noma, Umudike

8. Jami'ar Fasaha ta Modibbo Adama, Yola

9. Jami'ar Karatu daga gida NOUN

10. Makarantar Koyon Aikin Soji da Horas da Dakaru (NDA) Kaduna

11. Jami'ar Nnamdi Azikwe, Akwa

12. Jami'ar Obafemi Awolowo, Ile Ife

13. Jami'ar Abuja, Gwagwalada

14. Jami'ar Noma, Abeokuta

15. Jami'ar Noma, Makurdi

16. Jami'ar Benin, Edo

17. Jami'ar Calabar, Kogi

18. Jami'ar Ibadan, Oyo

19. Jami'ar Ilorin, Kwara

20. Jami'ar Jos, Jos

21. Jami'ar Legas, Akoko

22. Jami'ar Maiduguri, Maiduguri

23. Jami'ar Najeriya, Nsukka

24. Jami'ar Fatakwal, Rivers

25. Jami'ar Uyo, Uyo

26. Jami'ar Usmanu Dan Fodio, Sokoto

27. Jami'ar Tarayya Lafia, Nasarawa

28. Jami'ar Tarayya, Ndufu-alike

29. Jami'ar Tarayya Dutse, Jigawa

30. Jami'ar Tarayya ta Ma'adanan Man Fetur, Effurum

31. Jami'ar Tarayya, Oye- Ekiti

32. Jami'ar Fasaha ta Sojin Sama, Kaduna.

KARANTA KUMA: Jerin kasashen Afrika 10 da hasken wutar lantarki ya wadata

Ga jerin Jami'o'in Gwamnatin Jiha da aka bai wa lasisin karatun digiri na gaba a Najeriya:

1. Jami’ar Jihar Abia, Uturu

2. Jami'ar Jihar Adamawa , Mubi

3. Jami'ar Adekunle Ajasin, Akungba Akoko

4. Jami'ar Ambrose Alli, Ekpoma

5. Jami'ar Anambra, Uli

6. Jami'ar Jihar Benuwe, Makurdi

7. Jami'ar Fasaha ta Jihar Cross River, Calabar

8. Jami'ar Jihar Delta, Abraka

9. Jami'ar Jihar Ebonyi , Abakaliki

10. Jami'ar JIhar Ekiti, Ado Ekiti

11. Jami'ar Kimiya da Fasaha ta Jihar Enugu, Enugu

12. Jami'ar Jihar Imo, Owerri

13. Jami'ar Jihar Kogi, Anyigba

14. Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola, Ogbomoso

15. Jami'ar Jihar Legas, Ojo

16. Jami'ar Jihar Nasarawa, Keffi

17. Jami'ar Neja Delta, Wilberforce Island

18. Jami'ar Olabisi Onabanjo, Ago Iwoye

19. Jami'ar Kimiya da Fasaha ta Jihar Rivers

20. Jami'ar Umaru Musa Yar’Adua, Katsina

21. Jami'ar Jihar Gombe, Gombe

22. Jami'ar Ibrahim Babangida, Lapai

23. Jami'ar Kimiya da Fasaha ta Jihar Kano

24. Jami'ar Kimiya da Fasaha ta Jihar Kebbi

25. Jami'ar Jihar Kwara, Malete

26. Jami'ar Jihar Kaduna, Kaduna

27. Jami'ar Jihar Bauchi, Gadau

28. Jami'ar Jihar Yobe, Damaturu

29. Jami'ar Ilimi ta Ignatius Ajuru, Rumuolumeni

30. Jami'ar Ilimi ta Tai Solarin

31. Jami'ar Jihar Osun, Osogbo

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Ga jerin Jami'o'in masu zaman kansu da aka bai wa lasisin karatun digiri na gaba a Najeriya:

1. Jami'ar Kimiya da Fasaha ta Afirka, Abuja

2. Jami'ar Amurka ta Najeriya, Yola

3. Jami'ar Babcock, Ilishan Remo

4. Jami'ar Benson Idahosa, Benin

5. Jami'ar Bowen, Iwo

6. Jami'ar Covenant, Ota

7. Jami'ar Igbinedion, Okada

8. Jami'ar Pan-African, Lekki

9. Jami'ar Redeemers, Mowe, Ogun

10. Jami'ar Caleb, Legas

11. Jami'ar Joseph Ayo Babalola, Ikeji-Arakeji

12. Jami'ar Nile, Abuja

13. Jami'ar Afe Babalola, Ado Ekiti

14. Jami'ar Lead City, Ibadan (Digiri na biyu kadai)

15. Jami'ar Mkar, Mkar (Digiri na biyu kadai)

16. Jami'ar Madona, Okija

17. Jami'ar Al-Hikmah University, Ilorin (Digiri na biyu kadai)

18. Jami'ar Godfrey Okoye, Ugwuomu-Nike, Jihar Enugu

19. Jami'ar Adeleke, Ede

20. Jami'ar Veritas, Abuja

21. Jami'ar Achievers, Owo

22. Jami'ar Al-Qalam, Katsina

23. Jami'ar Baze, Abuja

24. Jami'ar Bells ta Kimiya, Ota

25. Jami'ar Crawford, Igbesa

26. Jami'ar Crescent, Abeokuta

27. Jami'ar Fountain, Osogbo

28. Jami'ar Landmark, Omu-Aran

29. Jami'ar Novena, Ogume

30. Jami'ar Salem, Lokoja

31. Jami'ar Bingham, Karu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel