Jerin kasashen Afrika 10 da hasken wutar lantarki ya wadata

Jerin kasashen Afrika 10 da hasken wutar lantarki ya wadata

- Najeriya ba ta cikin jerin kasashe 10 na Afirka da wutar lantarki ta wadata

- A wallafar da shafin Africa Facts Zone, ya yi, ya nun kasar Mauritius da Tunisia su na samun wuta dari bisa dari

- Kasar Ghana da Afrika ta Kudu sun shiga cikin jerin kasashen da hasken lantarki ya wadata

A yanzu kuma shafin nan na Africa Facts Zone, ya sake fitar da wata sabuwar kididdiga kan sha'ani da al'amuran da suka shafi kasashen nahiyar Afirka.

A wannan karo, shafin ya tattaro jerin kasashen nahiyar guda goma mafi samun wadataccen hasken wutar lantarki.

Jerin kasashen Afrika 10 da hasken wutar lantarki ya wadata
Jerin kasashen Afrika 10 da hasken wutar lantarki ya wadata
Asali: Facebook

Cikin jerin, kasar Mauritius da Tunisia sun ja ragamar kasashen da suka kere kowace kasa samun hasken lantarki dari bisa dari.

Haka nan kuma ba a bar kasar Masar, Algeria, Morocco da Seychelles a baya ba, inda sai an kai ruwa rana kafin hasken lantarki ya yi raurawa a kasashen.

KARANTA KUMA: Bayan shekaru shida da rasuwar Sarki Ado Bayero, an yi taron addu'a a fadar masarautar Kano

A jerin kasashen guda goma, babu kasar da ke samun hasken lantarki na kasa da kashi 80 cikin dari.

Kasar Afrika ta Kudu da kuma Ghana, su ma sun shiga cikin sahun kasashen goma na nahiyar Afirka da su ka yi zarra ta fuskar wadatuwa da hasken wutar lantarki.

Ga dai jerin kasashen guda goma da kuma kashi na daidaituwar da hasken wutar lantarki ya yi kowanne daga cikin su:

1. Mauritius, Tunisia (100%)

3. Egypt (99.8%)

4. Algeria (99.1%)

5. Morocco (99%)

6. Seychelles (99%)

7. Cape Verde (96.1%)

8. Gabon (90.7%)

9. Ghana (84.3%)

10. Afrika ta Kudu (84.2%).

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa, rashin wadataccen makamashin gas, da kuma karancin kayan aiki sun janyo raguwar karfin wutar lantarki a kasar nan daga ma'aunin megawatts 3,993.65 zuwa 3,608.

DUBA WANNAN: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wata sanarwa da ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya fitar, ya ce bangaren wutar lantarki ya yi asarar fiye da N2, 162,000,000 saboda raguwar karfin wutar a kasar.

Haka kuma a watan Janairun 2020 ne hukumar da ke sa ido a kan samar da hasken lantarki a Najeriya NERC, ta ce za a kara wa 'yan Najeriya kudin wutar lantarki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel