Kungiyar NAAC ta nemi Buhari ya sauke shugabannin tsaro domin ceto Najeriya

Kungiyar NAAC ta nemi Buhari ya sauke shugabannin tsaro domin ceto Najeriya

Kungiyar NAAC ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta fatattakar shugabannin tsaro domin ceto Najeriya da kuma gwamnatinsa daga abin kunya.

Kungiyar mai kare hakkin bil Adama, ta bai wa shugaba Buhari wannan shawara ne domin ya kubutar da gwamnatinsa daga kuncin zubar da jinin da masu tayar da kayar baya ke ci gaba da yin sanadi a kasar.

Shugaban gudanarwa na kungiyar, Dr Yusuf Kazeem, shi ne ya bayyana cikin jawaban da ya gabatar yayin taron manema labarai a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

Dr Kazeem ya ce, ci gaba da barin akalar tsaro a hannun su, wadda a yanzu babu sauran wata dabara da ta rage musu, babbar matsala ce da za ta haifar da koma baya ga tsarin tsaro a kasar.

Kungiyar ta yi zargin cewa, wata kitimurmura ce ta masu rike da madafan iko a fadar shugaban kasa, ita ta hana a tsige shugabannin tsaron saboda wasu dalilai na son rai.

Shugaba Buhari tare da shugabannin tsaro
Shugaba Buhari tare da shugabannin tsaro
Asali: Facebook

Ta ce wasu 'yan tsiraru masu ta-cewa a fadar gwamnatin kasar nan su ne suke fifita son zuciyarsu a madadin samar da ingataccen tsaro a Najeriya.

“Hujjoji na yau da kullum da muke samu sun nuna cewa, shugabannin tsaro sun yi rauni.

"Babu wani sabon abu da za su iya kawo da zai kara karfi a yaƙin da ake yi da masu tayar da zaune tsaye, 'yan fashi da sauran ababe na ta'ada."

KARANTA KUMA: Matawalle ya rantsar da sabbin kantomomi 14 a jihar Zamfara

"Sai dai shugabannin tsaron sun buge da kirkirar rahotannin karya da neman sauya tunanin al'umma wajen na nuna cewa an samu nasara a fagen yaki da ta'addanci a Najeriya."

"Su na hada kai da masu rike da madafan iko a gwamnati wajen yada farfaganda ta hanyar amfani da kafofin yada labarai domin sauya ra'ayin duniya a kan lamarin tsaron kasar nan."

"Abin takaici ne a ce kullum ana sadaukar da rayukan matasan dakaru, inda da suke ci gaba da kwanta dama a hannun 'yan ta'adda da sauran masu tayar da zaune tsaye."

Ya kamata a dawo daga rakiyar yin shiru gami da kauracewa kame baki a wannan lokaci duba da yadda ran mutum ya ke da tsadar gaske. "Dole ne shugaba Buhari ya yi abin da ya dace a yanzu."

"Kuma za mu ci gaba da amfani da muryoyinmu wajen yaye mayafin da aka yafawa Buhari da ke hana shi sanin rashin gaskiyar da ake tafkawa da sunan yaki da ta'addanci a kasar nan."

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Ta kara da cewa, an kashe daruruwan mutane a jihohin Kaduna, Katsina, Sakkwato da Zamfara da sauran wurare a cikin ‘yan kwanakin nan duk da ikirarin da sojojin ke yi na cin galaba a kan masu tayar da zaune tsaye.

Domin tabbatar da shugaba Buhari ya mike tsaye wajen sauke nauyin tsare rayuka da dukiyoyin al'umma, kungiyar ta sha alwashin gudanar da zanga-zanga nan ba jimawa.

Kungiyar za ta gudanar da zanga-zanga domin duniya ta farga a kan irin wasan kwaikwayon da shugabannin tsaron Najeriya ke yi wajen boye gazawarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel