Boko Haram: Yadda dimuwa da rashin kwanciyar hankali yasa 'yan ta'adda suke tarwatsewa

Boko Haram: Yadda dimuwa da rashin kwanciyar hankali yasa 'yan ta'adda suke tarwatsewa

Bayan matsa lambar da dakarun sojin Najeriya suka yi wa mayakan Boko Haram da ISWAP, da yawa daga cikin 'yan ta'addan sun fara gudun hijira.

A wata takarda da shugaban fannin yada labarai na rundunar, John Enenche ya bayyana, ya ce wasu daga cikin 'yan ta'addan da suka mika kansu ga rundunar sun tabbatar da cewa sansaninsu a rikice yake.

Enenche ya kara da bayyana cewa, rundunar sansanin soji da ke Konduga a jihar Borno tare da hadin guiwar 'yan sa kai na jihar Borno, sun kai wa 'yan Boko Haram da ke Lawanti hari inda suka kashe 6 yayin da sauran suka tsere da harbin bindiga.

Kamar yadda takardar ta bayyana, an samu miyagun makamai na 'yan ta'addan da suka hada da bindigar harbo jirgi daya, AK 47 biyu da harsasan harbo jirage.

Amma kuma, daya daga cikin dakarun ya rasa ransa yayin da daya ya samu raunika.

Takardar ta ce: "Bayan ci gaba da kai wa mayakan ta'addancin samame a maboyarsu, wasu daga ciki suna ta mika wuya ga dakarun sojin Operation Lafiya Dole.

"A ranar 2 ga watan Yunin 2020, 3 daga cikin 'yan ta'addan sun mika wuya a Pulka da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Su ukun sun tabbatar da cewa sun tsero daga sansaninsu ne da ke kauyen Dabulari da ke karamar hukumar Bama ta jihar Borno bayan ruwan wutar da suka sha. Mayakan da yawa sun rasa rayukansu.

"Sun bayyana nadamarsu a kan ayyukansu tare da kira ga sauran da su mika wuya don tseratar da rayukansu.

"A wani ci gaba makamancin hakan, a ranar 2 ga watan Yunin 2020 ne rundunar hadin guiwa ta birged ta 19 tare da runduna ta musamman ta 401 suka kai samame dajin Doron Naira da Magaji.

"A Doron Naira, dakarun sun samu littafin addini daya, harsashin harbo jiragen sama daya da kuma waya nadaddiya daya, wadanda mayakan suka gudu suka bari kafin isar dakarun.

"Hakazalika, a Daban Magaji, rundunar ta yi arba da mayakan ta'addancin inda ta shafe su a wurin. Sun halaka 9 daga ciki yayin da suka samu wasu makaman.

"Amma kuma soja daya ya riga mu gidan gaskiya yayin da daya ya samu rauni. An mika shi asibitin sojoji don samun kulawa".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel