'Yan Boko Haram sun ci gaba da mika wuya yayin da Sojoji ke musu kisan kare dangi - DHQ

'Yan Boko Haram sun ci gaba da mika wuya yayin da Sojoji ke musu kisan kare dangi - DHQ

A yayin ci gaba da tsananta ayyukan kakkabe ta'addanci a yankin Arewa maso Gabas, 'yan Boko Haram sun ci gaba da mika wuya yayin da Sojoji ke musu kisan kare dangi.

A ranar 3 ga watan Yuni, rundunar sojin kasa ta musamman da ke Konduga a jihar Borno tare da hadin gwiwar rundunar sa-kai, sun kai wani simame sansanin 'yan ta'adda da ke gabar Kogin Lawanti.

Rayukan 'yan kungiyar Boko Haram masu tayar da kayar baya 6 sun salwanta, yayin da dama suka tsere da raunuka na harbin bindiga.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin babban jami'in tsare-tsare na rundunar sojin kasa na kasa baki daya, Manjo Janar John Enenche.

'Yan Boko Haram sun ci gaba da mika wuya yayin da Sojoji ke musu kisan kare dangi - DHQ
'Yan Boko Haram sun ci gaba da mika wuya yayin da Sojoji ke musu kisan kare dangi - DHQ
Asali: Twitter

A cewarsa, wasu mayakan Boko Haram 3 sun zub da makamai tare da mika wuya, gami da bayyana huro wutar da dakaru ke musu a matsayin dalilinsu na saduda.

Mayakan uku, Mohammed Babagana, Modu Jugudun da Alhaji Usman, sun mika wuya ga dakarun da ke kula da yankin Pulka a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun kashe mutane 21, sun jikkata 12 a wani sabon hari da ya auku a kauyukan Zamfara

Sun bayyana nadamarsu da cewa wutar da dakaru ke hurowa a baya-bayan nan ta salwantar da rayukan da dama daga cikin abokansu, lamarin da suka ce gwara su mika wuya a madadin su yi mutuwar da babu riba.

Haka kuma a ranar 2 ga watan Yuni, hadin gwiwar dakaru na musamman sun tsefe sansanin masu tayar da kayar baya da ke Doron Naira da kuma Daban Magaji.

Bayan kawar 'yan ta'adda 9 da doron kasa, dakarun sun kuma tsinto muggan makamai da wasu daga cikin mayakan Boko Haram suka gudu suka bari a Daban Magaji.

Sai dai an yi rashin sa'a soja daya ya kwanta dama yayin da wani sojan daya ya jikkata.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

A ranar 1 ga watan Yuni, bataliyar sojoji da ke kula da yankin Madagali a jihar Adamawa, ta kakkabe sansanin 'yan Boko Haram a garin Lemu, Gajinji da Tsakiraku.

Yayin wannan tsifa da rundunar sojin ta gudanar, ta kawar da dan ta'adda daya sannan ta kama wasu mata biyu; Aishatu Manye da Kelune Mate.

An ruwaito cewa matan biyu sun kasance masu dakin wasu kwamandun Boko Haram ne a yankin.

Shugaban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya yaba da kwazon sojojin musamman juriyar su, jarunta da kuma jajircewa wajen kare mutuncin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel