Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa

Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa

- Kamar yadda mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a fannin yada labarai ya sanar, gobara ta tashi a Aso Villa

- Al'amarin ya faru ne a ranar Alhamis inda wata ma'adanar kayayyaki da ke kusa da majami'ar fadar ta kama da wuta

- Gobarar bata ci rai ba don tun kafin zuwan kwararrun masu kashe gobara aka fara kai dauki

Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa a garin Abuja a ranar Alhamis, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Babban mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya kwatanta gobarar da karamar gobara.

Hadimin shugaban kasar, ya ce al'amarin ya faru a ranar Alhamis inda wata ma'adanar kayayyaki da ke kusa da cocin fadar ta kama da wuta.

Ya ce: "Al'amarin ya faru ne sakamakon wutar lantarki wanda da gaggawa aka kashe tun kafin zuwan masu kashe gobara da ke wajen farfajiyar.

"Abun farinciki shine yadda babu wanda ya samu rauni kuma gobarar ba ta zama gagaruma ba."

Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa
Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa. Hoto daga Pulse.ng
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, hukumar kula da 'yan gudun hijira a ranar Alhamis ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta gina gidaje 500 don 'yan gudun hijira da ke jihohin Zamfara, Borno, Adamawa da Katsina.

Kwamishinan tarayya da ke kula da hukumar, Basheer Mohammed, ya sanar da hakan a garin Gusau yayin raba kayan tallafi ga 'yan gudun hijira a jihar. Mohammed ya ce, gwamnatin tarayya ta matukar damuwa da halin da 'yan gudun hijira miliyan 2.4 ke ciki.

Tana tunanin hanyar samar musu da matsuguni ta yadda za su yi rayuwa kamar kowa.

"Mun zo raba kayayyakin abinci da wadanda ba na abinci ba don amfanin jama'ar Anka, Gusau, Maradun, Shinkafi da Zurmi.

"A matsayinmu na cibiyar gwamnati, muna bada fifiko ne wurin bada kariya ga rayukan jama'ar da ke jihohi 36 har da babban birnin tarayya.

“Hukumar ta yi alkawarin gina gidaje 500 a jihohin Borno, Katsina, Adamawa da Zamfara a kashin farko na tallafin.

“Mun samu tabbaci daga jihohin Borno, Katsina da Adamawa cewa za mu samu hekta 50 ta fili.

"Hakan zai sa jama'a su koma garuruwansu sannan rayuwa ta koma kamar yadda take a da," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng