COVID-19: Camfi 9 da ake yadawa game da cutar korona

COVID-19: Camfi 9 da ake yadawa game da cutar korona

Idan mutum na bibiyar kafafen sada zumuntar zaman, kusan kowa magana yake a kan cutar korona. Barkewar cutar a fadin duniya ce ta kasance kanun labarai.

Amma kuma, har yanzu cutar sabuwa a wurin jama'a. Akwai labarai na kanzon kurege da na bogi da suka yawaita a yanar gizo game da cutar.

A don haka , akwai matukar amfani mutum ya tantance gaskiya da akasinta game da cutar. Ga camfi 9 da ake yadawa game da cutar a Afrika.

1. Sauro suna yada cutar korona: Wannan zance ne mara tushe balle makama don bashi da tushe a kimiyyance.

2. Amfani da magunguna irin su hydroxychloroquine na kashe kwayar cutar: Wannan ba gaskiya bane don har a halin yanzu babu maganin da cibiyar kiwon lafiya ta tabbatar da yana kashe kwayar cutar.

3. Man ridi a shafa a dukkan jiki, fitsarin yara da magungunan gargajiya na bada kariya daga cutar: Wannan zance ne mara tushe balle makama.

4. Siyan kaya da kasar China a kawo su inda mutum yake zai debo cutar: Tsawon dadewar da kaya ke dauka a hanya ba zai bar kwayar cutar ta rayu ba.

5. Kananan yara basu iya kamuwa da cutar korona: Wannan ba gaskiya bane. Hatta jarirai sabbin haihuwa na iya kamuwa da cutar. Cutar bata san shekaru ba.

6. Cutar korona ta hadin kai ce tsakanin manyan kamfanonin magani na duniya: Babu kamshin gaskiya a wannan al'amari.

7. Cutar korona makami ce da aka saki don karar da wasu jama'a: Babu gaskiya a cikin wannan zance.

8. 5G ne ya samar da korona ko kuma yake assasa cutar: Babu wata dangantaka a kimiyyance tsakanin 5G da annobar.

9. Korona cuta ce da aka bullo da ita don durkusar da wasu jama'a (Babu gaskiya a wannan al'amari.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa suka bayyana na ranar 3 ga watan Yunin 2020, an samu karin mutum 348 da ke dauke da cutar korona a Najeriya.

Kamar yadda ta bayyana, a jihar Legas an samu karin mutum 163, babban birnin tarayya an zakulo karin mutum 76 yayin da jihar Ebonyi ke da karin mutum 23.

Jihar Ribas na da karin mutum 21 sai jihohin Delta, Nasarawa da Niger ke da karin mutum takwas-takwas.

Jihar Enugu da ke kudancin Najeriya na da karin mutum 6 sai jihohin Bauchi, Edo, Ekiti, Ondo da Gombe sun samu karin mutum biyar-biyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel