Ofishin kasafi: N9b aka ware domin gyara ginin Majalisar Tarayya ba N27b ba

Ofishin kasafi: N9b aka ware domin gyara ginin Majalisar Tarayya ba N27b ba

Ofishin kasafin kudin kasa ya bayyana cewa, naira biliyan 9.25 aka sanya za a kashe wajen gyara ginin Majalisar Dokoki ta Tarayya a cikin kasafin kudin kasar na bana.

Darakta Janar na ofishin, Ben Akabueze, shi na ya kawar da wannan shakku a ranar Alhamis kan rahotanni da ke yaduwa game da shirin gyara gine-ginen Majalisun Tarayyar.

Ya ce kason da aka kayyade na gyara ginin Majalisar Tarayya, wanda a baya aka sanya naira biliyan 37, an zaftare shi da kashi 75 cikin 100.

Ya ce yanzu naira biliyan 9.25 shi ne adadin da aka sanya domin aiwatar da wannan aiki sabanin naira biliyan 27 da wasu rahotanni suka ambato.

Akabueze ya ce an rage kashi 75 cikin 100 daga kasafin gyara ginin majalisar sanadiyar mummunan tasirin da annobar korana ta haddasa a kudaden shiga da gwamnati ke samu.

Ya kuma ce kasafin kudin hukumar kula da karatun bai-daya (UBE) da na asusun kananan ma'aikatun kiwon lafiya ko kadan ba a taba shi ba.

Darakta Janar na Ofishin kasafi; Ben Akabueze da shugaba Muhammadu Buhari
Darakta Janar na Ofishin kasafi; Ben Akabueze da shugaba Muhammadu Buhari
Asali: UGC

Sai dai ya ce an daidaita kasafin ma'aikatun biyu don dacewa da kashi daya na asusun kudaden shiga kamar yadda doka ta tanada.

A watan Dasumba na 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin bana na naira tiriliyan 10.5, sai dai tasirin da annobar korona ta yi ya sa an gudanar da sauye-sauye a cikinsa.

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamnatin tarayya ta zabtare kasafin kudin gyara ginin majalisar dokokin tarayya da kusan naira biliyan 10.

KARANTA KUMA: Matasa sun hana tsohon soja ya kashe kansa a jihar Taraba

Gwamnatin kasar yayin gabatar da tsarin kwaskwarimar da ta yi wa kasafin kudin bana a ranar Talata, ta yanke naira biliyan 9.3 daga kasafin gyara ginin majalisun tarayya.

Tun a bara, naira biliyan 37 da aka sanya cikin kasafin na bana domin gyara ginin majalisar, ya janyo cece-kuce gami da suka daga bangarori da dama a fadin kasar.

Galibin 'yan Najeriya sun ce wannan ba komai ba ne illa barnar kudi da almundahana sannan kwata-kwata ba ya kan tsarin lura da halin da ake ciki.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Biyo bayan karyewar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya da kuma hasashen raguwar kudaden shiga da gwamnati za ta samu, ya sanya ta zaftare wani kaso daga kasafin da ta kiyasta.

A ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya mika wa majalisar tarayya sabon kudirin yi wa kasafin kudin kasar kwaskwarima, kuma wannan kudiri ya na kan gaba ta karatu na biyu.

Buhari ya yi bayanin cewa, kwaskwarimar ta zama dole saboda kifewar farashin mai da kuma rage adadin danyen mai da kasar ke fitar wa, wanda duk annobar korona ce ta yi sanadi.

A sabon kudirin yi wa kasafin kudin kwaskwarima, ga sauyin da za a yi wa kasafin Majalisar Dokoki ta Tarayya, Ma'aikatar lafiya da kuma Ma'aikatar ilimi:

An yanke kashi 25.1 cikin 100 daga naira biliyan 37 da aka sanya za a gyara ginin Majalisar Dokoki, inda a yanzu adadin kudin ya koma naira biliyan 27.7

Sai kuma asusun kananan ma'aikatun kiwon lafiya na kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar, an zaftare kashi 42.5 cikin dari, daga naira biliyan 44.5 zuwa naira biliyan 25.5 kacal.

Haka zalika, an rage kashi 54.25 cikin dari na kasafin kudin hukumar kula da karatun bai-daya UBE, daga naira biliyan 111.7 zuwa naira biliyan 51.1.

Duka duka dai an cire kashi 10 cikin 100 na kasafin kudin majalisar dokokin tarayya, daga naira biliyan 128 zuwa naira biliyan 115.2.

Hakan ta ke ga ma'aikatar shari'a ta kasa, wadda ita ma aka zaftare kashi 10 cikin 100 daga kasafin kudinta. A baya an sanya mata naira biliyan 110, yayin da yanzu ya dawo naira biliyan 99.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel