Hoton wasu 'yan 6 da suka kammala karatun sakandire ya zagaya yanar gizo cikin sauri

Hoton wasu 'yan 6 da suka kammala karatun sakandire ya zagaya yanar gizo cikin sauri

- 'Yan shidan iyalin Harris a birnin Birmingham na kasar Birtaniya, sun kammala Makarantar Sakandire a garin Alabama na kasar Amurka

- Mata biyu; Kaylynne da Kiera, da kuma Maza hudu; Kaleb, Kobe, Kieran da Kyle, sun kammala Makarantar Sakandiren Center Point a Amurka

- Wani ma'abocin dandalin sada zumunta, Ferlando Parker Sr., ya taya 'yan shidan murnar kammala wannan mataki na karatunsu a yanar gizo

Wasu 'yan shida iyalan Harris da ke birnin Birmingham na kasar Birtaniya, sun kammala karatunsu na Sakandire a Makarantar Center Point High da ke garin Alabama a Amurka.

Labarin mai ban al'ajabi na wannan 'yan shida sananne ne tun yayin da aka haife su kuma Mai Duka ya raya su cikin koshin lafiya.

Biyo bayan wannan abun a yaba musu da suka yi na kammala wani mataki na karatu, a yanzu sun sake daukan hankalin al'umma.

Iyalan mazauna birnin Birmingham da Mai Duka ya azurta da 'yan shida rigis, an yi ta yamudidi da rahotonsu yayin da suka haihu a ranar 8 ga watan Yulin 2002.

Sun taba bayyana a wani shirin gidan Talbijin mai taken The Oprah Show a watan Afrilun 2007.

Ma'auratan biyu; Diamond da Chris Harris, sun yi haifi jariran ne, mata biyu; Kaylynne da Kiera, da kuma Maza hudu; Kaleb, Kobe, Kieran da Kyle.

Chris da matarsa Diamond, sun samu wannan tabarraki bayan amfani da wasu magunguna masu taimaka wa wajen samun juna biyu.

Tun a shekarar 2001 jaridar Dailymail ta ruwaito cewa, ma'auratan sun yi ta faman neman samun haihuwa domin su fara tara iyali amma lamarin ya ci tura.

Diamond ta samu haihuwa a aurenta na fari, kuma 'danta, Dewayne a yanzu ya kai shekaru biyar.

Fiye da shekaru biyu bayan aurensu da Chris, Likitoci suka bai wa Diamond shawarar shan wasu kwayoyin magani masu karfafa samun juna biyu.

KARANTA KUMA: Da yiwuwar za a dawo da zirga-zirga tsakanin jihohi a ranar 21 ga watan Yuni - Sani Aliyu

Ba jimawa, Diamond ta dauki ciki, kuma Likitoci suka shaida mata abun alheri da samun 'yan tagwaye. Sai dai bayan an matsa bincike an gano cewa 'ya'ya biyar za ta haifa.

A ranar 8 ga watan Yulin 2008, Diamond ta haifi 'yan shida rigis wadanda su ne kadai 'yan shidan da aka taba haifa kuma suka rayu a tarihi.

A shekarar 2015 ne, matan; Kaylynne da Kiera da kuma mazan hudu; Kaleb, Kobe, Kieran da Kyle, suka yi bikin murnar cikarsu shekaru 13 a duniya.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Legit.ng ta zakulo hoton 'yan matan biyu da samarin hudu, wanda wani ma'abocin dandalin sada zumunta, Ferlando Parker Sr. ya sanya a yanar gizo.

Parker ya fadi burin da 'yan shidan suka sanya gaba a yanzu bayan kammala karatun Sakandire.

Kobe da Kalynne za su tafi jami'ar Jihar Alabama, yayin da Kaleb da Kieran za su wuce jami'ar Alabama A&M.

Kiera zai ci gaba da karatu a jami'ar Lawson State sai kuma Kylie zai karanci dabarun rayuwa a tsohuwar makarantarsu ta Center Point High.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel