Ke duniya: Matashi mai shekaru 25 ya yi wa tsohuwa mai shekaru 70 fyade

Ke duniya: Matashi mai shekaru 25 ya yi wa tsohuwa mai shekaru 70 fyade

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wani matashi mai suna Wasiu Bankole mai shekaru 25 a kan zarginsa da ake da yi wa tsohuwa mai shekaru 70 fyade.

Jami'ai daga ofishin 'yan sanda da ke Agbado a karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar ne suka damke shi a ranar Laraba, sa'o'i kadan bayan aikata laifin da yayi.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

Oyeyemi ya bayyana cewa, tsohuwar da aka yi wa fyade ce ta kai wa 'yan sandan kara, jaridar New Telegraph ta wallafa.

Ta ce tana bacci a gidanta a ranar Talata ne matashin ya balle kofa ya shigo tare da yin lalata da ita.

Ya ce: "An kama matashin bayan tsohuwa da yayi wa fyade ta kai kara. Ta ce tana bacci ya balle gidanta ya shigo a ranar Talata, 2 ga watan Yunin 2020 a yankin Abule Lemode da ke Ijoko.

"Ya shiga dakinta sannan ya yi lalata da ita ta karfi ba tare da amincewarta ba.

"Tsohuwar ta ce, daya daga cikin makwabtan ta ne ya ji kururuwarta sannan ya zo da sanda ya buga wa matashin.

Ke duniya: Matashi mai shekaru 25 ya yi wa tsohuwa mai shekaru 70 fyade
Ke duniya: Matashi mai shekaru 25 ya yi wa tsohuwa mai shekaru 70 fyade. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Hakan ne yasa ya tsere tare da barin kayansa, takalmi da tocila a dakinta.

"Bayan kai korafin, DPO din ofishin 'yan sandan, SP Kuranga Yero ya tura jami'ai don neman wanda ake zargin. Tuni suka cafko shi tare da mika shi ofishin 'yan sandan.

"Bayan tuhumarsa, ya amsa laifinsa amma ya ce giya ya sha a lokacin da ya aikata."

Oyeyemi ya ce an mika wanda ake zargin asibiti don duba kwakwalwarsa.

Ya kara da cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson, ya bada umarnin mika lamarin gaban sashen kare hakkin dan Adam da hana fasa-kwabrin kananan yara na sashin bincike na manyan laifuka na jihar don bincike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel