Babu wata kofa ta samun kudin shiga da cutar korona ba ta yi wa illa ba - Lai Mohammed

Babu wata kofa ta samun kudin shiga da cutar korona ba ta yi wa illa ba - Lai Mohammed

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce annobar cutar korona ta yi kane-kane a duk wata kafa mai ba da damar samun kudin shiga a fadin duniya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, gwamnatin kasar ta ce babu wata kofa ta samun kudin shiga da annobar korona ba ta yi wa mummunar illa ba a yanzu.

Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 3 ga watan Yuni.

Ministan Labarai da Al'adu; Lai Mohammed
Ministan Labarai da Al'adu; Lai Mohammed
Asali: Facebook

Furucin ministan ya zo ne a yayin amsa tambayoyi da korafe-korafen yadda kudin gudanar da muhimman ayyuka ya yanke wa ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati a kasar nan.

Ministan ya ce wannan kalubale ba a Najeriya kadai ake fuskantarsa ba, sai dai ko ina a fadin duniya ana fama da radadin da annobar korona ta haddasa.

KARANTA KUMA: Zaben Edo da Ondo: Babu wanda zai jefa ƙuri'a idan ba shi da takunkumin rufe fuska - INEC

A yanzu Najeriya tana fuskantar babbar matsala ta karancin samun kudaden shiga sakamakon karyewar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya.

Kalubalen da wannan matsala ta haifar shi ne ta yadda ba za a iya aiwatar da wasu muhimman ayyukan raya kasa da ke cikin kasafin kudin 2020 ba.

Babu ko tantama barkewar annobar korona ce ta haifar da nakasu da tawaya ga tattalin arziki a duniya baki daya.

Wannan dalili ya sanya dole kanwar naki ta tursasawa gwamnatin Najeriya aiwatar da sauye-sauye a kasafin kudin kasar na bana tun a watan Mayun da ya gabata.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Gwamnatin kasar ta zaftare kasafin kudinta na bana daga naira 10.59 zuwa naira tiriliyan 10.52 kamar yadda ministar kudi, kasafi, da tsare-tsare, Zainab Ahmed ta sanar.

Idan ba a manta ba, Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari ta yi karyewar da ta samu asarar kusan naira bilyan 350 tun a makon farko na watan Maris.

Dama dai ita Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari da bazar farashin danyen mai a duniya ta ke fankama. Tunda kuma farashin ya karye a duniya, to tilas ya shafi Najeriya ita ma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel