Coronavirus: WHO ta ci gaba da gwaji a kan Chloroquine

Coronavirus: WHO ta ci gaba da gwaji a kan Chloroquine

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce za ta ci gaba da gwaji a kan hydrochloroquine (maganin zazzabin cizon sauro), domin maganin cutar korona.

A ranar 22 ga watan Mayu, mujallar kiwon lafiya ta The Lancet, ta wallafa cewa maganin zazzabin cizon sauro (chloroquine) ba ya da tasiri wajen magance cutar korona.

The Lancet ta yi ikirarin cewa, chloroquine bai yi ingantaccen tasiri ba a kan mutane 96,032 masu cutar korona da aka yi gwajin maganin a kansu.

Kwanaki uku bayan wannan wallafa, Tedros Ghebreyesus, shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya, ya bada sanarwar a dakatar da gwaji a kan maganin na chloroquine.

Da yake jawabi a yayin wani taron manema labarai a ranar Laraba, Tedros ya ce a yanzu za a ci gaba da gwajin chloroquine a kokarin da ake yi na neman mafita ta cutar korona.

Ya ce binciken da kwamitin kula da lafiya na WHO ya gudanar ya gano cewa, babu wani dalili da zai sa a katse gwajin chloroquine bayan sake nazari da yin bita a kan maganin.

Tedros Ghebreyesus; shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya
Tedros Ghebreyesus; shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya
Asali: UGC

Tedros ya kara da cewa, a yanzu majalisar zartarwa ta hukumar ta ba da shawarar a ci gaba da gwaji gadan-gadan a kan maganin har sai an tabbatar da ingancinsa ko sabanin haka.

Tun a watan Maris ne shugaban kasar Amurka Donald Trump, yayi kira ga likitocin kasar da su rika ba mutane masu cutar korona maganin zazzabin cizon sauro wato dai chloroquine.

KARANTA KUMA: Jerin ɗakuna 9 na gidan kurkuku mafi alfarma a duniya

Kamar yadda sashen Hausa na jaridar Premium Times ya ruwaito, Trump ya ce an yi amfani da maganin a kasar Chana, kuma ma dai idan har bai yi aiki ba, ba zai kashe mutane ba.

Sai dai kuma a wancan lokacin Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, ba a gama bincike a kan maganin ba domin tabbatar da ko yana maganin cutar korona.

Nau'in maganin mai suna Chloroquine phosphate shi ne wanda aka fi amfani da shi a nahiyar Afirka musamman a shekarun 1980 da 1990.

Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar China ce ta bayyana hakan.

Gidan talbijin na China Global Television Network ya ruwaito cewa daukacin masana a kasar sun amince a yi amfani da Chloroquine phosphate domin maganin cutar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel