Cutar korona ta hallaka mutum 7 a jihar Gombe - Prof. Idris Mohammed

Cutar korona ta hallaka mutum 7 a jihar Gombe - Prof. Idris Mohammed

Kwamitin kar ta kwana da gwamnatin jihar Gombe ta kafa domin lura da annobar cutar korona, ta ce a halin yanzu an samu mutum 7 da cutar ta hallaka a fadin jihar.

Farfesa Idris Muhammad, shugaban kwamitin, shi ne ya sanar da hakan cikin birnin Gombe yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba, 3 ga watan Yuni.

A baya Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito mutuwar mutane uku, sai kuma daga bisani aka sake samun mutum hudu da cutar korona ta yi sanadiyar ajalinsu.

Farfesa Muhammad ya ce mutum uku cikin bakwai din da suka riga mu gidan gaskiya, sun kamu da cutar ne ba tare da sun fita daga cikin jihar ba.

A halin yanzu, mutum 23 ne kadai suka rage cikin masu cutar a jihar, kuma an ware su a cibiyar killace majinyata ta Asibitin Koyarwa da kuma cibiyar killace masu cutar da ke garin Kwadon.

Sai dai ya bayyana damuwa matuka dangane da yadda jama'a ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum a cikin jihar ba tare da nuna wata fargaba ba ta annobar.

Cutar korona ta hallaka mutum 7 a jihar Gombe - Prof. Idris Mohammed
Cutar korona ta hallaka mutum 7 a jihar Gombe - Prof. Idris Mohammed
Asali: UGC

Ya ce wannan mummunar dabi'a da al'ummar jihar suka tsira abar damuwa ce, duba da yadda ta ke mayar musu da hannun agogo baya wajen dakile yaduwar cutar.

Cutar korona wadda ta ke janyo sarkewar kafofin numfashi, ta hallaka akalla mutane 380,000 a fadin duniya kuma har yanzu likafarta na ci gaba.

KARANTA KUMA: Zaben Edo: Obaseki ya mayar da fam din bayyana ra'ayin takara hedikwatar APC

Yayin da wasu kasashe suka cimma wani munzali na samu damar shawo kan cutar, wasu na fama da ita musamman a nahiyar Afirka da Amurka Ta Kudu.

A nahiyar Afrika, akalla mutum 4,467 ne suka mutu kuma kasar Algeriya, Kamaru, Najeriya, Masar, Afrika ta kudu, Maroko da Sudan, su ne suka fi yin rashi mai girma.

A nan gida Najeriya, cutar ta hallaka mutane 314 a jihohi 29 kawo ranar Laraba, 3 ga watan Yuni, 2020, bisa la'akari da alkaluman da Hukumar hana Yaduwar Cututtuka a Najeriya, NCDC ta fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel