Zaben Edo: Obaseki ya mayar da fam din bayyana ra'ayin takara hedikwatar APC

Zaben Edo: Obaseki ya mayar da fam din bayyana ra'ayin takara hedikwatar APC

A yau Laraba, 3 ga watan Yuni, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya isa hedikwatar jam’iyyar APC domin gabatar da fam dinsa na bayyana ra'ayin takara.

Obaseki ya isa sakateriyar jam'iyyar da ke birnin Abuja cikin tawagar hadimai da dimbin magoya baya kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Bayan isowarsa, gwamnan ya afka ofishin babban sakataren tsare tsare na jam'iyar, Barrister Emma Ibediro inda ya gabatar da shaidarsa ta neman takara.

Sashen Hausa na jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Obaseki ya hakikance a kan sake neman takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a zaben da a za gudanar watan Satumba.

A jiya Talata, 2 ga watan Yuni, 2020, Mista Obaseki ya shaida cewa zai jarraba sa’arsa ne a zabe mai zuwa kuma a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC.

Yayin da wata kungiya ta Magoya baya wanda ake kira Obaseki Mandate Group ta kai wa gwamnan ziyara, ya shaidawa masoyan na sa cewa zai tsaya a cikin jam’iyyar APC.

Shugaban kasa Buhari tare da Obaseki rike da fam din bayyana ra'ayin takara na jam'iyyar APC
Shugaban kasa Buhari tare da Obaseki rike da fam din bayyana ra'ayin takara na jam'iyyar APC
Asali: Twitter

Idan ba ku manta ba a makon jiya ne wani jigo na PDP mai adawa a yankin kudancin Najeriya ya bayyana cewa kofa a bude ta ke ga gwamna Godwin Obaseki idan ya sauya sheka.

Emmanuel Ogidi ya yi wa Obaseki tayi ganin yadda ya ke fama da rikicin cikin gida. A karshe gwamnan ya yi fatali da wannan zawarci, ya ce a APC za a gwabza da shi.

KARANTA KUMA: Bai kamata farashin mai ya haura N70 ba a yanzu - PDP

Obaseki ya bayyana wa ‘yan Obaseki Mandate Group a jiya cewa, masoyansa a shirye su ke su da su siya masa fam din takara a kowace jam’iyyar siyasa da ya bukaci tsayawa takara.

Sai dai duk da wannan goyon baya da gwamnan mai-ci ya ke samu daga masoyansa, ya ce ya natsu da ya sake neman tikitin takara karkashin jam’iyyar da ta kawo shi kan mulki.

Rahotannin da mu ka samu daga jaridar Punch sun bayyana cewa gwamnan ya ji dadin yadda mutane su ka hada kudi, su ka saya masa fam din APC saboda ya cigaba da rike jihar.

A cewarsa ya shiga siyasa ne domin ya canzawa mutane ra’ayi na ganin cewa ‘yan siyasa mutane ne da ke neman mulki ta hanyar a mutu ko ayi rai, ya yi kira ga mutane su zabi na kwarai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel