Fallasar bidiyon batsa: Matar auren da ke ciki na yunkurin kashe kanta

Fallasar bidiyon batsa: Matar auren da ke ciki na yunkurin kashe kanta

Wata mata mai matsakaicin shekaru tana barazanar kashe kanta sakamakon fallasar bidiyonta ana lalata da ita.

Hakan yasa jama'ar yankin da take, suke zundenta tare da yi mata dariya.

Kamar yadda Adomonline.com ta ruwaito, an nadi bidiyon Maame Mary yayin da suke jima'i tare da wani mutum.

Bidiyon ya yadu a yankin, wanda hakan yasa jama'a suke zundenta tare da yi mata ba'a.

Fusatacciyar matar ta yi ikirarin cewa matashin ne ya ja ta wanda tun farko abokinta ne. Ta ce tashi daga bacci tayi ta ganta tare da shi a gado.

"Ya gayyaceni fita amma daga baya sai na gane cewa na bugu ne. Washegari, na ganni kwance tare da shi a gado. Daga baya na gane cewa ya nadi bidiyon abinda ya faru tsakaninmu kuma ya tura wa abokansa," ta labarta.

Maame Mary ta ce wannan al'amarin ya kusa kashe mata aure amma mijinta ya yi namijin kokari ta yadda ya yi hakuri.

Ta kai karar lamarin ga 'yan sanda amma kamar yadda tace, 'yan sandan sun ja mishi kunne kawai ba tare da daukar mataki ba.

An gano cewa, Maame Mary na yunkurin kashe kanta don kare martabar mijinta. Ana zundensu tare da yi musu ba'a da nuna kyama ga iyalanta.

Fallasar bidiyon batsa: Matar auren da ke ciki na yunkurin kashe kanta
Fallasar bidiyon batsa: Matar auren da ke ciki na yunkurin kashe kanta. Hoto daga The Pulse
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Babban asirin Boko Haram ya tonu a Borno - DHQ

A wani bidiyo na daban, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jagoranci raba kayayyakin abinci da wadanda ba na abinci ba ga gidaje 10,000 a Rann, hedkwatar Kala-Balge.

Wannan ziyarar ce ta hudu da gwamnan ke kai wa karamar hukumar da ke da iyaka da jamhuriyar Kamaru.

Jirgin dakarun sojin saman Najeriya ne ya dauka Zulum daga Maiduguri zuwa Rann a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2020.

Gwamnan da ya yi irin tafiyar har sau uku, na farko a watan Yunin 2019, kwanaki kadan bayan hawansa mulkin jihar don duba yanayin ayyukan da ake yi a yankin.

A watan Disamban 2019, ya koma garin inda ya raba wa mata masu takaba kudi N15,000 kowannensu.

Zulum ya sake komawa Kala-Balge a watan Fabrairun shekarar nan don raba naira miliyan 100 ga iyalai 10,000 da ke yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel