Najeriya ta na bayanka - Buhari ya tabbatar wa shugaban bankin Afrika, Adesina

Najeriya ta na bayanka - Buhari ya tabbatar wa shugaban bankin Afrika, Adesina

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya za ta tsaya tsayin daka wajen goyon bayan Dakta Akinwumi Adesina a kokarin sa na sake zama shugaban bankin ci gaban Afirka, AfDB.

Hakan ya fito ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina.

Cikin sanarwar da Mista Femi ya gabatar, ya ce Buhari ya bayar da tabbacin ne a fadarsa ta Abuja, a ranar Talata yayin da ya karbi bakuncin Dr Adesina wanda ya kai masa ziyarar ban girma.

Buhari ya yi alkawarin cewa, Najeriya za ta hada kai tare da sauran shugabanni da masu ruwa da tsaki a bankin AfDB don ganin an sake zabar Dakta Adesina a wa’adi na biyu.

Shugaban kasar ya ce zai yi hakan ne duba da tubalin nasarorin da Dakta Adesina ya kafa a wa'adin mulkinsa na farko.

Ya tunasar da Dakta Adesina rawar da ya taka wadda ta tabbatar da nasararsa ta kasancewa shugaban bankin AfDB (African Development Bank).

Yayin da Buhari yake ganawa da shugaban bankin Afrika, Akinwumi Adesina
Yayin da Buhari yake ganawa da shugaban bankin Afrika, Akinwumi Adesina
Asali: Twitter

Yana mai cewa: "A shekarar 2015, lokacin da ake batun zaben ka a karon farko, na rubuta wa dukkan shugabannin Afirka wasika, na ba su shawarar cancantarka da wannan matsayi."

"Kasancewar ka mutumin da ya rike kujerar minista a jam'iyyar adawa ta PDP, hakan bai hana ni goyon bayanka ba duk da na kasance a jam'iyyar APC."

A nasa furucin, Dakta Adesina ya yi wa shugaba Buhari ta'aziyar mutuwar tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Marigayi Abba Kyari.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta umarci manyan ma’aikatan su koma aiki daga yau Talata

Ya kuma bayyana magajin Kyari, Farfesa Ibrahim Gambari, a matsayin “mutum mai gaskiya da bajimi a idon duniya."

A baya-bayan nan ne aka hurowa Dakta Adesina wuta ta zargin nuna bangaranci da wariya wajen nade-naden manyan mukamai a bankin AfDB.

Sai dai hukumar gudanarwa ta bankin ta wanke Adesina da zargin da ake masa, lamarin da ta ce ba za ta nemi ya sauka daga mukaminsa ba.

Mai magana da yawun bankin, Niale Kaba, ta ce babu wata matsalar shugabanci ko ta tsarin mulki a bankin.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, masu kwarmata bayanai ne suka zargi Mr Adesina da nada 'yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel