Hamshakan masu kudin duniya 20 a shekarar 2020 (Hotuna)
Annobar korona ta shafi duk wani bangare na tattalin arzikin duniya da kasuwanci. Amma duk da haka, mujallar Forbes ta wallafa manyan masu kudi a duniya da suka kai 2,095.
Ga manyan masu kudin duniya 20 da takaitaccen bayani a kansu.
1. Jeff Bezos: Dan asalin kasar Amurka ne kuma ya samu kudinsa ta fasahar Amazon. Bezos ya mallaki dukiya da ta kai $113 biliyan. Shine ya fi kowanne mahaluki kudi a duniya a shekarar 2020.

Asali: Facebook
2. Bill Gates: Dan asalin kasar Amurka ne kuma shi ke da fasahar Microsoft. Bill Gates ya mallaki dukiyar da ta kai $98 biliyan kuma shine mutum na biyu da ya fi kowa arziki a duniya a 2020.

Asali: Getty Images
3. Bernard Arnault & Family: Hamshakin mai kudin ya mallaki dukiyar da ta kai $76 biliyan kuma dan kasar Faransa ne.

Asali: Getty Images
4. Warren Buffett: Hamshakin mai arzikin ya mallaki dukjya da ta kai $67.5 biliyan. Dan asalin kasar Amurka ne mamallakin Berkshire Hathaway Finance & Investment.

Asali: Getty Images
5. Larry Ellison: Mai tarin dukiya ne da ya bayyana a mataki na biyar a fadin duniya. Ya mallaki dukiyar da ta kai $57 biliyan. Dan asalin kasar Amurka ne.

Asali: Getty Images
6. Amancio Ortega: Mashahurin mai arzikin ya mallaki kudi da suka kai $55.1 biliyan. Dan asalin kasar Spain din na da kamfanin Zara Fashion & Retail.

Asali: Getty Images
7. Mark Zuckerberg: Ya mallaki dukiya da ta kai $54.7 biliyan kuma dan asalin kasar Amurka ne. Shine ke da fasahar Facebook.

Asali: Facebook
8. Jim Walton: Ya mallaki dukiyar da ta kai $54.7 kuma dan asalin kasar Amurka ne. Shi ke da Walmart Fashion & Retail.

Asali: Twitter
9. Alice Walton: Ta mallaki dukiyar da ta kai $54.4 biliyan kuma 'yar asalin kasar Amurka ce.

Asali: Twitter
10. Ron Walton: Mashahurin mai arzikin ya mallaki dukiyar da ta kai $54.1 biliyan kuma dan asalin kasar Amurka ne.
KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
11. Steve Ballmer: Babban mai arziki ne a duniya da ya mallaki dukiyar da ta kai $52.7 biliyan. Dan kasar Amurkan ya dogara da fasahar Microsoft.

Asali: Getty Images
12. Carlos Slim Helu $ Family: Hamshakin mai arzikin dan asalin kasar Mexico ne kuma ya mallaki dukiyar da ta kai $52.1 biliyan. Ya dogara da arzikin fasahar sadarwa ne.

Asali: Getty Images
13. Larry Page: Hamshakin mai arzikin ya mallaki dukiyar da ta kai $50.9 biliyan kuma dan asalin kasar Amurka ne. Shi ke da fasahar Google.

Asali: Getty Images
14. Sergey Brin: Hamshakin mai arzikin ya mallaki dukiyar da ta kai $49.1 biliyan kuma dan asalin kasar Amurka ne.

Asali: Getty Images
15. Francoise Bettencourt Meyers & Family: Ta mallaki dukiyar da ta kai $48.9 biliyan. 'Yar asalin kasar Faransan taa dogara da kasuwancin L'Oreal Fashion & Retail.

Asali: Getty Images
16. Michael Bloomberg: Hamshakin mai kudin dan asalin kasar Amurka ne kuma ya mallaki dukiyar da ta kai $48 biliyan.

Asali: UGC
17. Jack Ma: Dan asalin kasar China ne wanda ya dogara da fasahar kasuwanci ta yanar gizo kuma dukiyarsa ta kai $38.8 biliyan.

Asali: UGC
18. Charles Koch: Ya mallaki dukiyar da ta kai $38.2 biliya. Dan asalin kasar Amurkan ne mamallakin Koch Industries.

Asali: Getty Images
19. Julia Koch & Family: Kasuwancin da silar azikin da ya kai $38.2 biliyan ta dogara ne da Koch Industries a kasar Amurka.

Asali: Getty Images
20. Ma Huateng: Dan asalin kasar Chinan ya dogara da fasahar yada labarai ta yanar gizo. Ya mallaki dukiyar da ta kai $38.1 biliyan.

Asali: Getty Images
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng