Gwamnatin Tarayya ta umarci manyan ma’aikata su koma aiki daga yau Talata

Gwamnatin Tarayya ta umarci manyan ma’aikata su koma aiki daga yau Talata

- Gwamnatin Najeriya ta umarci manyan ma’aikatan gwamnati daga mataki na 14 zuwa sama da su koma bakin aiki gadan-gadan

- Wannan umarni ya fito ne daga bakin shugaban ma'aikatan gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan

- Esan ta bayyana cewa, ma’aikatan gwamnati da ke kula da ayyukan a muhimman bangarori su gaggauta koma wa aiki kai tsaye

A yunkurin sassauta dokar kullen da aka shimfida saboda annobar korona, Gwamnatin Tarayya ta umarci manyan ma'aikatan gwamnati su koma aiki gadan-gadan.

Gwamnatin Tarayya ta umarci manyan ma'aikata da ke mataki na 14 zuwa sama, da su koma bakin aiki daga yau Talata, 2 ga watan Yuni.

Umarnin da Gwamnatin ta yi ya fito ne daga bakin shugaban ma'aikatan gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Folasade, ta ba da wannan umarni cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai.

Ta umarci dukkanin ma'aikata da ke ayyuka a muhimman bangarori na gwamnati da su gaggauta komawa bakin aiki.

Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya; Folasade Yemi-Esan
Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya; Folasade Yemi-Esan
Asali: UGC

Ta yi bayanin cewa, ma'aikatan za su rika fita aiki a kullum tun daga ranar Litinin zuwa Juma'a daga karfe 9.00 na safe zuwa 2.00 na rana.

KARANTA KUMA: Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin AfDB, Adesina

Folasade ta kuma shawarci ma'aikatan da su tabbatar sun kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta domin dakile yaduwar cutar korona.

A karshe, ta nemi cibiyoyi da ma'aikatun gwamnati su takaita yawan baki da za su rika karba gwargwadon iko, tare da tabbatar da kowane bako ya kiyaye matakan da hukumomin lafiya suka gindaya.

Haka kuma, Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Legas, a yau Talata ta ba da umarnin sakin tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, daga kurkuku.

A ranar 5 ga watan Dasumba, 2019, aka yankewa Mista Kalu hukuncin zaman shekaru 12 a gidan dan Kande.

Hakan ya biyo bayan samunsa da laifin yin ruf da ciki a kan N7.1bn tare da kamfaninsa, Slok Nigeria Limited, da kuma wani tsohon Daraktan Kudi a gwamnatin Jihar Abia, Jones Udeogu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel