Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin AfDB, Adesina

Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin AfDB, Adesina

A yanzu dinnan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga bayan labule tare da shugaban bankin Afrika, Dr Akinwumi Adesina, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin Mista Adesina tare da shugaban ma'aikatan fadar shugabna kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, inda suka shiga ganawa gadan-gadan.

Sauran manyan jami'an gwamntain tarayya da suka gana da Mista Adesina tare da shugaba Buhari sun hadar da Ministar Kudi, Kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed.

Sai kuma Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffery Onyeama, mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina da sauransu.

Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin AfDB, Adesina
Hakkin mallakar hoto: TVC News
Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin AfDB, Adesina Hakkin mallakar hoto: TVC News
Asali: Twitter

AfDB, cibiyar hadin gwiwa ce mallakin kasashen Afirka wadda kasar Amurka ta kasance babbar mai hannun jari a cikinta.

Shugaba Buhari da sauran shugabannin Afirka, na ci gaba nuna goyon baya a kan Adesina, wanda zai cika wa’adinsa kuma yana da damar a sabunta shi na wani tsawon shekaru biyar.

A baya-bayan nan ne aka hurowa Mista Adesina wuta ta zargin nuna bangaranci da wariya wajen nade-naden manyan mukamai a bankin ci gaban Afirka, African Development Bank (AfDB).

KARANTA KUMA: Kasashe 11 a Afrika da suka fi tara mutane masu ilimi

Sai dai hukumar gudanarwa ta bankin ta wanke Adesina da zargin da ake masa, lamarin da ta ce ba za ta nemi ya sauka daga mukaminsa ba.

Mai magana da yawun bankin, Niale Kaba, ta ce babu wata matsalar shugabanci ko ta tsarin mulki a bankin.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, masu kwarmata bayanai ne suka zargi Mr Adesina da nada 'yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa.

A bangare daya kuma Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, Majalisar wakilai ta tarayya, ta amincewa shugaba Buhari karbo bashin $22.7bn daga kasar waje.

'Yan majalisar sun amince da karbo bashin ne yayin zaman majalisar da ya gudana a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, bayan jin ta bakin kwamitin basussuka na majalisar.

Sai dai wasu 'yan majalisar musamman na yankin Kudu maso Yamma, sun nuna rashin amincewarsu da hakan, lamari da suka ce yankinsu ba ya da rabo a ayyukan da za'ayi da kudin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel