Kisan mahaifi: Kotu ta yanke wa wani magidanci hukuncin kisa

Kisan mahaifi: Kotu ta yanke wa wani magidanci hukuncin kisa

Wata kotun laifuka na musamman da ke Ikeja a ranar Litinin ta yankewa wani mutum mai suna Rasak Abiona hukuncin kisa.

Kotun ta zargi Abiona da lakadawa mahaifinsa mai shekaru 62 mugun duka da rodi a yayin da suka samu sa'in'sa a garin Legas.

A hukuncin da aka yanke, Mai shari'a Oluwatoyin Taiwo ya ce, duk da lauyan mai kare kansa ya bada shaidu masu yawa amma kotun ta bincika tare da gano cewa wanda ake zargin ne ya kashe mahaifinsa.

"Wannan mummunan al'amari ne yadda da ya kashe mahaifinsa," Alkalin da ya kama Rasak da laifin kisan kai yace.

"Babu shakka ya so kashe mahaifinsa tunda ya buga mishi rodi a kai.

"Wanda ke kare kansan zai iya gamsar sa mahaifinsa mai shekaru 62 a kan ko mene ne ba tare da buga mishi rodi a kai ba.

"Wannan babban bayani ne a kan abinda fushi da rashin hakuri za su iya kai mutum. A don haka na yanke mishi hukuncin kisa sakamakon kashe mahaifinsa Sunday Abiona," alkalin yace.

A farko, lauyan wanda ake zargin, Obinna Mbagho ya roki kotun da ta rangwanta wa wanda yake karewa don wannan ne karo na farko da ya taba aikata laifin kuma ya nuna nadama.

"Ya kasance a gidan gyaran hali tun 2013 tunda aka fara shari'ar, 'ya'yansa duk sun watse," Mbagho yace.

A yayin sukar rokon, mai gabatar da kara, Olakunle Ligali, ya bukaci kotun da ta hukunta wanda ake zargin da hukuncin da ya dace.

Kisan mahaifi: Kotu ta yanke wa wani magidanci hukuncin kisa
Kisan mahaifi: Kotu ta yanke wa wani magidanci hukuncin kisa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ikon Allah: Yadda aka samu shugabannin kasa 2, gwamnoni 4 da ministoci 2 a aji daya

Kamar yadda mai gabatar da kara ya bayyana, Rasak ya kashe mahaifinsa a ranar Lahadi, 28 ga watan Fabrairun 2012 a gidan mamacin da ke lamba 22 titin Taiwo da ke Ejigbo a jihar Legas.

A yayin shari'ar, an samu shaidu biyar da suka hada da dan uwansa, Lanre Abiona da kuma kanninsa mata biyu, Kafilat Abiona da Shakirat Abiona.

Sauran shaidun sun hada da Dr Moses Akpeniyi da dan sanda mai bincike, ASP Fsetus Omoru.

Wanda ke kare kansa bai kira wata shaida ba don karfafa ikirarinsa.

Kamar yadda Lanre ya sanar, Rasak ya saba dukan mahaifinsu. Akwai lokacin da ya duke shi har hakoransa suka zube.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel