Ikon Allah: Yadda aka samu shugabannin kasa 2, gwamnoni 4 da ministoci 2 a aji daya

Ikon Allah: Yadda aka samu shugabannin kasa 2, gwamnoni 4 da ministoci 2 a aji daya

Kwalejin gwamnati da ke Bida, jihar Neja makaranta ce mai babban tarihi. An kafa ta a 1912 kuma tana da tarihin yaye 'yan Najeriya masu tsananin nasara a fannoni daban-daban na rayuwa.

Amma ajin shekarar 1957 zuwa 1962 na makarantar na cike da abubuwan al'ajabi.

Ya samar da soji 7 masu mukamin Janar da kuma Kanal daya.

Biyu daga cikin Janar din sun shugabanci Najeriya, hudu daga ciki kuwa sun yi gwamnoni sai sauran biyun sun kai mukamin ministoci.

Daga hoton 'yan aji, mutum mai lamba 21 shine Janar Gado Nasko, mai lamba 23 kuwa Janar Sani Sami ne yayin da dalibi mai lamba 9 ya zama Janar Ibrahim Babangida.

Dalibi mai lamba 10 Janar Garba Duba ne, dalibi mai lamba 13 kuwa Kanal Sani Bello sai dalibi mai lamba 16 ya zama Janar Abdulsalam Abubakar.

Dalibi mai lamba 3 Janar Mohammed Magoro ne, dalibi mai lamba 6 marigayi Janar Mamman Vatsa ne.

Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar sun kai matakin shugabannin kasar Najeriya.

Ikon Allah: Yadda aka samu shugabannin kasa 2, gwamnoni 4 da ministoci 2 a aji daya
Ikon Allah: Yadda aka samu shugabannin kasa 2, gwamnoni 4 da ministoci 2 a aji daya. Hoto daga TheNigeriaToday
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali ya angwance

Manjo Janar Gado Nasko ya taka matsayin gwamnan jihar Sokoto, Laftanal Janar Garba Duba ya taka matsayin gwamnan jihar Bauchi da kuma mai mulkar jihar Sokoto sai kuma Kanal Sani Bello ya zama gwamnan jihar Kano.

Birgediya Mohammed Sani Sami, wanda shine sarkin Zuru a yanzu ya taka matsayin gwamnan jihar Bauchi tsakanin watan Janairu na 1984 zuwa watan Augustan 1985, a yayin mulkin Manjo Janar Muhammadu Buhari.

Manjo Janar Mohammed Magoro ya taka matsayin Ministan harkokin cikin gida a lokacin mulkin Manjo Janar Muhammadu Buhari, yayin da Janar Mamman Vatsa ya kai matsayin Ministan babban birnin tarayya.

A ranar 5 ga watan Maris din 1986 ne aka yanke mishi hukunci a karkashin gwamnatin dan ajinsu, Janar Ibrahim Babangida, sakamakon wani juyin mulki da suka shirya amma basu samu nasara ba.

Kwalejin gwamnatin ta Bida wacce aka sani da Provincial Secondary School Bida tana da babban tarihi.

A fannin shari'a, ta yaye tsohon alkalin alkalai Idris Legbo Kutigi, Jastis Ndajiwo da Jastis Abdullahi Mustapha.

A fannin diflomasiyya, ta samar da marigayi ambasada James Tsado Kolo, Ambasada Buba, Ambasada Yunusa Paiko da Ambasada Abdulrahman Gara.

A fannin siyasa, kwalejin ta samar da manyan mutane irinsu Farfesa Jerry Gana, Sanata Awaisu Kuta, Ibrahim Tanko da Isa Mohammed Waziri.

A fannin malumta akwai Farfesa Musa Abdullahi, Mohammed Dakota, A. I Kolo da M. T. A Suleiman.

A fannin sarauta akwai Malam Auwal Ibrahim, sarkin Kontagora, Alhaji Saidu Namaska, sarkin Nupawa da sarkin zuru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel