Duk wanda ya taba bani cin hanci ya fito ya fallasa - Ministan Buhari ya caccaki 'yan Najeriya

Duk wanda ya taba bani cin hanci ya fito ya fallasa - Ministan Buhari ya caccaki 'yan Najeriya

- Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika, ya ce bai taba karbar cin hanci ba ko kuma bukatar hakan ba

- Ya bayyana cewa, duk wanda ke da bayani mabanbanci da hakan da ya gaggauta fitowa don fallasa shi a idon duniya

- Ya yi wannan martanin ga 'yan Najeriya bayan ma'abota amfani da twitter sun caccake shi tare da zargin suna karbar rashawa kafin barin jirgi ya tashi

Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, ya ce bai taba karbar cin hanci ko bukatar hakan ba. Ya kalubalanci duk wanda ke da wani bayani mabanbancin hakan da ya fito ya bayyana.

A ranar Litinin, Sirika ya ce wannan bayanin ya zama dole sakamakon caccakarsa da 'yan Najeriya ke yi a Twitter.

Sun zargi ma'aikatar sufurin jiragen saman da bukatar cin hanci kafin su amince da tashin jiragen sama yayin barkewar annobar nan.

A yayin jawabi ga kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona a Abuja, ya ce wannan ikirarin ba gaskiya bane.

"Na karanta a shafin Twitter cewa akwai wasu kudi da muke karba kafin amincewa da tashin jiragen sama. Wannan al'amari ya nisanta daga gaskiya. Kyauta ne kuma amince wa ake yi," yace.

Duk wanda ya taba bani cin hanci ya fito ya fallasa - Ministan Buhari ya caccaki 'yan Najeriya
Duk wanda ya taba bani cin hanci ya fito ya fallasa - Ministan Buhari ya caccaki 'yan Najeriya. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Cashewar matan aure a gaban mazansu: Mawaki Hamisu Breaker ya yi karin haske

"Ko sakon kar ta kwana ka tura, za mu tura maka na amincewar mu. Kada wanda ya bata wa wani suna kuma mutane su daina tuna baya.

"Mu a wannan gwamnatin, muna daukar ayyukan da suka shafe mu da muhimmanci. Shekaru na biyar ina minista kuma na kalubalanci duk wanda ya ji wannan.

"Babu wani ma'aikacin mu da ya mallaki jirgin kansa ko kamfanin jiragen sama ko kuma yake kasuwancin abinci, otal ko motar haya a filayen jirgin.

"Duk wanda ke da wata shaida a ma'aikatar nan, tun daga sakatare, darakta ko ma'aikacin gwamnati na cewa na bukata ko na karba kudi daga ko waye, ya fito ya sanar," ministan ya kalubalanta.

Ministan ya shawarci 'yan kasa da su daina rayuwar tuna baya don kuwa gwamnatin Buhari ta bambanta daga ta sauran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: